Salihan mata, masu da’a ne, masu tsare gaibi saboda abin da Allah Ya yi umarni a kiyaye
Wadannan siffofi guda biyu: da’a da tsare abin da Allah Ya yi umarnin a tsare, su ne sinadaran zama da miji; su ne lakanin da za ki yi amfani da su don ki zama matar da mijinki zai rika so a kullum; su ne siffofin salihar mace, wacce Manzon Allah SAW Ya siffanta da mafi kyawu. Idan kina so ki zama haka ga maigidanki ya ’yar uwa sai ki yi kokari ki cika wadannan kyawawan siffofi na macen kwarai, kamar yadda Allah SWT Ya bayyana, domin Shi Ya halitta ’ya mace, Ya fita sanin mafi kyawun abin da zai kyautata na daga dabi’a da yanayin zamantakewa. Don haka sai ki yi amfani da wadannan sinadaran kamar yadda bayaninsu zai zo
da’a: Yin da’a ga maigida ba yana nufin yi masa ladabi da biyayya kadai ba, duk da cewa suna ciki; yin da’a ga maigida ya kunshi har da salo-salon bayyanar da soyayya gare shi, da yi masa abubuwan jan hankali. Ki lura da yadda kayan sarrafa sha’awa na mata ake masu lakani da ‘kayan da’a.’ Ga bayani kan ire-iren da’ar da za ki rika yi wa maigidanki, musamman a wannan lokaci na bankwana da masoyin wata na Ramadan da kuma gabatowar shagalin Sallah, don ya kasance kin ribaci dimbin ladan da ke ciki.
Ladabi Da Biyayya Wannan shi ne tozon da’ar da za ki yi wa maigidanki, duk wata da’a da za ki yi masa, idan har ba ki yi masa ladabi da biyayya ba, to wannan da’a za ta zama mai nakasu kwarai da gaske. Amma in kina masa ladabi da biyayya, ko da ba ki yi masa sauran bangarorin da’a ba, ladabi da biyayya na iya sakaya inda kike da rauni har ba za a lura ba ki yin su ba ma
Ladabi- shi ne yin amfani da hankali wajen kiyaye duk abin da kika san maigidanki ba ya so, sannan ki rika yin hakuri da tausasa zuciyarki wajen bin dokokinsa sau da kafa; sannan yana daga cikin ladabi ki rika girmama mijinki da kankan da kai gare shi, rashin raina shi ko raina kokarinsa; rashin yi masa rashin kunya da gaya masa bakaken maganganu. Ladabi ne danne zuciyarki yayin da ya bata miki rai da nuna fushinki gare shi ta hanya mafi sauki
Biyayya ita ce bin umarninsa kodayaushe cikin halin kunci da na dadi, amma wannan a cikin umarnin da ba su saba wa dokokin Allah SWT ba. Kamar yadda Hausawa ke cewa: “yi na yi, bari na bari ta raba ka da kowa,” idan kika zama mai biyayya sau da kafa ga mijinki, to za ku zauna lafiya, ba za a taba jin kanku ba. Ki sani ya uwargida, ke ce ya dace ki yi masa biyayya, domin shi ne shugabanki, kina kasa da shi, kuma ke mallakinsa ce, don haka kada ki dauka cewa yin haka kaskanci ne gare ki, a’a, yin ladabi da biyayya babbar daraja ce gare ki, kuma ita ce cikar kamalarki ta ’ya mace
Duk macen da ba ta da ladabi da biyayya, to za ka tarar dabi’unta sun fi kama da na dabbobi sama da na mutane. Kuma idan kika iya sarrafa makaman kashe lakar da namiji da Ubangiji Ya hore miki, sai ya zama mijinki yana miki ladabi da biyayya ba tare da wai kin umarce shi da hakan ba, ko kin sa masa wasu dokoki
da’ar So Da kauna: Uwargida za ki yi wa maigidanki da’ar so da kauna iri biyu: na farko shi ne, ki yi tanadin so mai dumi da sahihiyar kauna cikin zuciyarki game da mijinki, hadi da sauran kyawawan shau’ukan ’yan rakiyar shau’kin so da kauna. Sannan sai ki rika bayyanar da wannan so da kaunar salo-salo a zahirance. Za ki yi haka ne ta hanyar jiji da shi, shagwaba shi da yi masa shagwaba, sannan kallonki da murnushinki gare shi su zama masu cike da so da kauna da jan hankali. Kin fi kowa sanin irin makaman jan hankalin da Ubangija ya ni’imta ki da su, don haka sai ki yi amfani da su wajen samun ladar auren ki wanda shi ne rabin addinin. Ki sani cewa, so, kauna da ingantacciyar kulawa ga juna su ne dadin rayuwar aure ba dukiya, daula da more rayuwar duniya ba. Don haka kodayaushe ki zama mai yawan sabunta salo-salon so da kaunar da za ki rika bayyanarwa ga maigidanki; ki yawaita yin masa abubuwan jin dadin da za su faranta masa rai.