Shayin Sobo da citta don Karin lafiya

Da farko Zan yi kira kadan da fatar a Ki yaye.
Masu ganin magunna na yawo a social media su kwasa su je su hada suna ta shan wasu hade haden da ba a san asalin su ba,to mu sani wasu abubuwan gubane ba magani bane komai ka sha a cikin cikinka yake tafiya ba tareda kana ganin irin illar da yake yima ba.Wani abun idan ka hada ka sha daga ranar ka rasa lafiya kenan.
Sai a kula da kyau.

Ka nemi citta busashe qwara uku masu kyau ka hada da Jan so6o shima busashe ka wanke sai ya wanku sai ka tafasa sai ya tafasa sosai,ka tsaye ruwan ga cup madaidaici sai ka tarfa Zuma cokali uku manya sai ka fifita sosai idan ya dan huce sai ka sha bayan an karya da kuma yamma bayan an ci abinci.
Wallahi wannan abun sha ne da yafi dukkanin kayan zaqin nan na kolba dana gwangwani da ake sha na drinks amfani nesa ba kusa ba.

magani ne da ke

Kara jinin jiki fiye da kowane irin abinci da wani abun sha.

Yana karawa jikin yara,maza da mata harma da tsofaffi lafiya da kuzari zaka rinka jin kanka garau a koyaushe.

Yana maganin cutukan huhu irin su tarin sanyi na mura,majina, tarin tibi,asma,tarin nimoniya da ciwon kirji,da kuarjen huhu da majinar kirji da ta daskare,da tarin bronchitis.

Yana wanke ciki da ya cushe saboda ciye ciye na kayan maiko da xaqi,yana magance kumburin ciki,tsuwar ciki,zafin ciki,yawan tusa,da yawan lalcewar ciki da tsutsar ciki da ciwon ciki,da yawan zuwa toilet,da sauran su.

Yana maganin cutukan fitsari waton urinary tract infections,kamar yawan fitsari da jin zafi yayin fitsari,da fitsarin jini,da kaikaiyin matse matsi,da cutukan sanyi da zauqewar zakari.

Yana Maganin cutukan jini,da kumburin jini,da ciwon ga6o6i da jiyojin jiki waton joint and muscle pain.

Yana maganin hauhawan jini da saukowar jini waton hypertension da kuma hypotension.

Yana wanke babbar hanzanya da lausasa bayan gari mai tauri da rage radadin ciwon basir mai tsiro.

Yana Maye gurbin karamcin sinadirrai masu samarwa jiki da isashen jini.

Yana karawa hanta lafiya da kare cutukan koda.

Yana karawa masu HIV karfin jiki da kuzari kuma yana rage kaimin ciwon tsida waton Aids.

Yana sa kiba ga mata da maza masu sirrantaka na jiki da bana halitta ba.

A jarraba za ayi matukar jin dadin wannan maganin.

Da fatar Allah ya sa mu amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *