SHAWARWARI GA MA’AURATA

TAMBAYA?

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Malam dan Allah inada wata tambaya tsawon shekarana shidda da aure kenan amma har yanzu bamu fahimci juna da mijina ba.

Da wahala muyi wata guda ba tare da wata matsala ba. Nayi iyakar yina amma bai taɓa fahimtata ba.

  • Na soshi domin Allah.
  • Ina bashi hakkinsa na kwanciya.
  • kirkii, biyaya, addu,a Duk babu wanda bana yi, amma har yanzu babu jituwa sosai.

Kuma mu biyu ne amma sai ya dinga nuna man banbanci atsakani, idan nayi masa magana sai ya nuna man yana sona kuma da zarar lokacin ya wuce shikenan.

Malam dan allah kaban shawara.

AMSA

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

kin san shi zaman aure ibada ne. Kuma ita ibadah, zaka bauta wa Allah ne ta yadda Allah ɗin yake so, ba dole sai yadda kai kake so ba.

Don haka abinda Allah keso gareki azaman aure shine wannan da kikeyi ɗin :

Ladabi da biyayya.
Ki bawa mijinki hakkinsa na aure. Hakuri da juriya idan an samu Saɓani. Addu’a da kulawa da ibadah.

Shawarar da zan baki anan ita ce:

  • idan kin san kina da saurin fushi, to ya kamata ki yayyafa wa zuciyarki ruwan sanyi ki dena bayyna fushi ko yin magana cikin fushi. Domin fushi karshensa nadama ne.
  • Idan kin san kina da saurin mayar masa da martani alokacin da duk yake cikin fushi, to ki dena. Ki koyi yin shuru koda kuwa kece kike da gaskiya acikin rikici.
  • Idan kin san kina da yawan zargi ko gori, to ki dena. Domin mafiya yawan maza suna tsanar mace mai yawan zargi, da kuma mai yawan gori bayan tayi wani abun alkhairi.

Namiji yakan kasa mancewa da gori ko baqar magana har tsawon lokaci, haka zukatan wasu mazan take.

Ki koyi kyautata masa fiye da kishiyarki koda shi ya munana miki alokacin. Domin Allah yana son masu kyautatawa asanda aka chutar dasu kuma suke da ikon mayar da martani.

  • Idan kin san kina yawan tuhumarsa kamar yana nuna fifiko atsakaninki da abokiyar zamanki, to ki dena. Domin ayanayin halayyar zama, akwai wanda ba ya son mace mai tseewa da surutu da kwarototo koda shine yayi mata laifi, bazai taɓa gyarawa ba, sai dai ma ya Qara tsanarta.

Amma idan kika bishi ahankali, kina hakuri kuma kina kyautata masa, da sannu insha Allahu shi da kansa zai gyara kuma ya dawo yana jin kunyarki, yana jin nauyinki, kuma zai ji kunyar munana miki koda abayan idonki ne.

Sannan ki Qara tsafta bisa wacce kike da ita, sannan ki Qara kyautata kwalliya da girki.. Duk waɗannan suna ɗaukar hankalin namiji sosai.

Sai kuma sauran halastattun hanyoyin da zaki iya bi wajen Qara shiga zuciyarsa waɗanda kin fini saninsu. (ina nufin irin su tarairaya, shagwaba, da sauransu).

WALLAHU A’ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *