SHAWAR-WARI 20 GA MATA MASU JUNA BIYU

Ki baiwa abunda ke cikin ki kulawa matuka, saboda kisami lafiya da kubuta keda abinda ke cikinki ta hanyar daukar cikin da mahimmanci

Ki rika cin abinci sosai, irin wanda yake gina jiki (proteins irinsu; kifi, kwai, wake, alala, nama dss), ta yanda zaki sami lafiya tare da abunda ke ciki.

Ki rika cin kayan mar-mari, kamar su kwad’on rama, cucumber, karas cabbage ko latas da makamantansu a kowace rana.

Ki rika shan kaman kofi biyu na madara, ko nono a kowace rana inhakan ya samu

Kada ki rika shan Tea me Nescafe, Bournvita, Milo ko ovaltine, Sai Tea me madara kurum ko kuma asha empty da citta da lipton……… saboda su bournvita na kumbura yaro aciki zakisha wuya wajen naquda koma akai ga sai anyi aiki anciro dan.

Kada ki rika shan magani daka ba tare da shawartan likita ba, saboda hakan zaki iya cutar da abunda ke cikinki…saboda wani maganin na ratsawa har cikin mahaifa… ciki kuwa hadda maganin gargajiya… shyasa ake haifo wasu yaran da karamin kai, ko datsattsen lebe da hanci

Yana da kyau a rage saduwa da Iyali, lokacin da ciki yake awatanni ukun farko, da kuma watanni biyun karshe na haihuwa, yawan aikata hakan yana tasiri ga lafiyarki da ta Yaron. Sannan a watanni ukun farko hakan na iya haddasa zubewar cikin…yayin da watanni biyun karshe hakan na iya jawo naquda ba shiri ki haifi jariri bakwaini.

Ki rika bacci isashshen domin rashin yin barci da wuri zeke sanya miki damuwa da yawan kasala… don haka dole ne kikeyin barci na Awa tara a kowace rana, a tsawon lokacin goyon cikin.

Kada ki rika yin aiki me wahala da d’aga abubuwa masu nauyi, domin hakan ze Iya samar da matsala ga cikin.

Ki lazimci Natsuwa da rashin fushi, sakamakon wasu matsaloli na gida, ko na Y’an Uwa, saboda ki samu kwanciyar hankali, ana buk’atan hakan dan cikin ya kasance yadda akeso, batare da wata matsala ba.

Kada ki rika ziyartan marasa lafiya, masu dauke da ciwon da za’a iya kamuwa dashi, don ze zama hatsari agareki da kuma jaririnki.

Kada ki rika sanya tufafi masu matse jiki, ko daure ciki da k’arfi tsawon yayin goyon cikin domin yin hakan ze saki gajiya, da shan wahala wajen yin numfashi tare da hajijiya

Kada ki rika sanya takalma masu tsini ko tudu domin hakan zai sabbaba rashin walawa a ga6obin jikinki, wanda hakan ze samaki ciwon baya

Dolene ki rika yawan ziyartan likita akai-akai, tsawon lokacin goyon ciki, Sau d’aya cikin kowani wata musamman cikin wata na shida, da kuma sau d’aya cikin kowanne sati biyu a wata na bakwai dana takwas, da kuma sau daya cikin kowanne sati a watana tara har zuwa lokacin haihuwa.

Ki rika neman abaki gwajin jini dana fitsari kinayi, lokaci zuwa lokaci saboda ki tabbatar cewa jikinki baya dauke da wani ciwo da yaron ze iya kamuwa dashi, kaman ciwon sugar, ciwon hanta da makamantansu.

Dole ne ki dinga yin wanka a kowacce rana sau 1 zuwa 2 ko 3 aduk lokacin tsawon goyon ciki, da lokacin shayarwa, dan ki kare lafiyarki, da na yaronki

Ki rika kula da nononki tun daga wata na biyar da samun ciki saboda shayar da danki nono na asali wato cholesterol… ganganci ne awatanni haihuwa me gida ya rika tsotson nonon mace saboda colostrum din da ake so yaron ya samu ka iya tahowa a irin wannan lokacin… in tsotso yai yawa

Ki rika tafiya da k’afa a kowace rana gwargwadon iyawarki cikin gidanki…wato kaiwa da komowo kamar taku 300 hakan ze kyautata miki jinin jiki lokaci zuwa lokaci yadda zai zama abinci ga danki kuma ya sauwak’e maki wahala yayin haihuwa.

Ana son haihuwa a asibiti, saboda samun kulawarki data jaririnki, kuma babu laifi ki haihu a gida idan har kin shawarci likitarki ta tabbatar miki da cewa duk abinda ya shafeki da d’an yana tafiya daidai, kuma tai alkawarin zuwa ta tsaya kanki yayin nakuda harki haihu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *