SAKONNIN SOYAYYA ZUWA GA MASOYI/MASOYIYA SAURAYI/BUDURWA MIJI DA MATA

Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin ciki na, ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari.

Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina Son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan ta’ba mantawa da su ba har abada a rayuwata. ki huta lafiya.

Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya.

Ina son ka. Ka kula min da kanka. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda d’aya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.

Komai na mu ya kasance yana faruwa ne a lokaci guda hatta ba’kin ciki da kuma farin-ciki, wato ruhi d`aya gangar jiki kuma biyu. Farin cikin ki shi ne nawa, ina son ki.

Tausayi da tausasawa su ake kira “so” kowa yana da wacce yake so, Ni ke nake so. Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba.

Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *