SAHIHAN BAYANAI GAME DA ABUBUWAN DA SUKESA GABAN MACE BUDEWA

 1. Yawan jima’i baisa gaban Mace ya Buɗe. Da yawa kan yaɗa cewa yawan jima’i nasa Mace buɗewa!, amma sam wannan ba gaskiya bane, daga shekarun Mace sai haihuwa sune kaɗai ke tasiri wajen buɗe wannan gurin.
 2. Shan abarba bai ƙarawa Mace zaqi ko daɗi wajen mu’amala, ko kuwa sa gaban Mace irin ƙamshinta. Babu wani binkicen ilimi da ya tabbatar da hakan
 3. Ba duk farin ruwa ne don anga yana fita daga Mace ba za’a ce ciwon sanyi ko infections ne ba. Kwai lokutan da ruwa fari tas kamar nono kan riƙa fita wanda yake healthy ne, ko aga yayin jima’i fari me kauri na fitowa duk gefe da gefe har jikin halittar namijin kamar ya shafa farin cream ko kindirmo wannan bai nuna infections Normal ne, matukar ba ɗoyi sosai akaji yana yi ba haɗe da zafin jima’in. Amma haka kurum is normal seeing that.
 4. Ba rashin tsafta bane don lokaci zuwa lokaci Mace na jin gabanta na smell musamman In Mace tasan tana da tsaftar ta daidai gwargwado. Is normal, tun ma ba a Mata masu jiki sosai ba.
 5. Maza ya dace kusani ba’a taɓa iya ƙara tsayi ko kaurin azzakari. don haka ku dena wahalar banza tare da asarar kuɗi duk damfara ce, galibi daga shekara 19 highest zuwa 21 shikenan tsayi ya kammala. Saide ma ta ragu amma bade ka qarata ba.

Da yawa kan dami kansu bisa jin ana dole halittar namiji ta zamo qatuwa kafin Mace ta iya samun gamsuwa dashi… Amma wannan ma ba gaskiya bane, Size doesn’t matter for satisfaction, Galibi ya ta’allaqa da kwarewarka ne wajen tattaɓa Macen.

 1. Jiqa lemon tsami, kanwa ko Jiqa gishirin andir asha bayan kammala jima’i bai taɓa hana ciki shiga. Saide indama ba kwanakin shigar cikin bane dama.
 2. Akan ce inde Namiji bai release acan cikin Mace ba dab da Mahaifarta wai ciki bazai shiga ba. Amma wannan ba gaskiya bane! muddin gaban Namiji ya shiga an sami ɓuyan kan kaciyarsa toh ko bai shigar da sauran halittar ba… toh fa batun ace waje-waje yai release baida wani tasiri. Ciki na iya shiga, saide in ba kwanakin shigar nasa bane dama. Domin maniyyi shi ke kai kansa cikin mahaifa dama. Haka wani mutsu-mutsu ko mikewa bayan release duk bai hana ciki shiga.
 3. Wanke farji nan da nan bayan kammala jima’i ko sa hannu a riƙa janye ragowar ruwan da namiji ya zuba ana wankowa bai hana shigar ciki shima.
 4. Jima’i da Macen da Bata kai ga fara haila ba, ko kuwa Macen da karonta na farko data san Namiji duk bai hana Ciki shiga, Ciki na iya shiga matukar alamun cikar halitta sun bayyana koda bata soma haila ba, kuma koda saduwar farko kenan. Shyasa wasu daga fyaɗe zaku ga ciki wuff ya shiga
 5. Akan nuna kamar Magungunan hana ɗaukar ciki dole ana shan su ne nan take bayan gama jima’i.

Wannan ba gaskiya bane, don kurum ance emergency contraceptive pills Bai nufin Sai ansha nan da nan, kwai wanda ko bayan kwana uku da yin sex ne sannan aka sha bazai bar ciki ya shiga ba. Saide kurum shan akan kari yafi nutsuwa, zai kuma hana mantuwa.

 1. Bawani salon kwanciyar jima’i da don anyi zai hana ciki shiga. Ko a tsaye ake muddin namiji yai release jikin Mace ciki na iya shiga. Ba ruwan sperm da gravity, saide cire gravity din na taimakawa gudun sa.
 2. Jimawa ana jima’i ba shi ke tabbatar da daɗin jima’in ba ga wacce ake da ita. Da wasa da komi minti 7 zuwa 14 ya wadatar. Hasali 75% na Mata stimulation yafi gamsar dasu fiye da penetration don Allah Mahaukata cikin Maza ku daure ku ƙauracewa shaye-shayen magungunan ƙarin karfi, jima’i ilimi ne ba karfi ba.
 3. Da yawa kan zaci Mata kan ɗau lokaci kafin shaukin jima’i ya ratsa su su sakarwa namiji jiki, ko sha’awa ta taso musu… Amma wannan ba gaskiya bane, Babu wani bambanci tsakanin yadda namiji ko Mace ke saurin arousing ko kamuwa ya zaqu. Kurum wuyarta kowa yaga ko yaji ko ya sami abinda yake so… Shikenan
 4. Akan ce kallon halittar Mace kai tsaye nasa ka fahimci ko tasha kwantawa da Maza. Wannan ƙarya ne!
  Wannan abin na tsananin jawo zargi, haka kurum ace kallo ko shigar Mace na iya sa mutum ya fahimci inma Macensa na kwanciya da wasu ko kuwa wani ya taɓa saninta. Wannan kuskure ne babu wani abu irin wannan shi farji elastic ne kamar robali yana stretching, haka rashin ganin jini bai nuna tabbas Mace ta taɓa sanin namiji.

Kamar yadda nace Haihuwa ce kadai in Mace ta taɓa yi shine likitoci ke iya ganewa da kallonta, koda angyarata, inba likita ba bame gane haka. Kuma koshi haihuwa mukan gane bawai kurum kace Mace na saduwa ba

 1. Don Namiji bai iya ya jima ba a jima’inku na farko, ko daren farko ba…. Wannan bai nuna yana da Matsala kokuwa ragone a shimfiɗa.

A lura da kyau sabbin aure! Da yawa an gurɓata tunaninku ta hanyar kallon videos din batsa da novels. Amma nasha faɗa jima’in Minti 3 zuwa 5 acikin Mace in a cire foreplay is still perfect.

Shi jima’i a hankali ake kwarewa, kowacce Mace yadda jikin Namiji ke jin ta daban, a hankali ake har azo sanda jimawar zata qaru, tamkar wanda yasai sabuwar samfurin wayar kamfanin da bai taɓa riƙe irinta bane, sai a hankali kake qara fahimtar ta. Ba’a cewa ana da matsalar saurin released har sai anyi wata 6 batare da anga canji ba. Sannan za’a fara tunanin magana.

 1. Babu wata alaqa tsakanin girman halittar namiji da wani sashi nasa. Misali ace duk mai babban tafin ƙafa ko hanci, yatsa yana da girman halitta… Haka girman bakin Mace da halittarta ko wani abu. Wannan ba wani binkice da ya nuna haka, kurum saide coincidence.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *