SABULUN WANKA MUSAMMAN GA BAKAR MACE DOMIN GYARAN FATA

Asamu

sabulun salo ko
sabulun Ghana
magiji.
Zuma
lemun tsami.
zaitun

a hada sabulun Ghana da magiji a dake a zuba Zuma a matsa lemun tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son tayi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau.

GYARAN FUSKA AMMA NA SABULU

sabulun salo
sabulun Zuma
Zuma
aloevera
man zaitun
kwakwa

a Samu sabulun salo ko sabulun Ghana kamar girma sabulun giv guda biyu, a Samu sabulun Zuma guda daya idan ba’a sameshi ba asa aloevera soap, a daka sabulun ko a goge asa ruwan ganyen aloevera cokali uku, Zuma cokali uku,an zaitun cokali daya, man kwakwa cokali daya, a hada a kwaba, a dinga shafawa a fuska, bayan minti goma ko sha biyar sai a wanke fuskar yana saka kyan fuskar tayi shaining tayi kyau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *