Alhamdulillah abin nema ya samu yadda musulunci ya kara samun karuwar wata yar uwa data karbi musulunci sakamakon yadda ta bayyana cewa addinin musulunci yana matukar burgeta da kuma yadda taga musulmai suna matukar kaunar junan su, koda kuwa basusan juna ba a zahiri.
Matar ta bayyana cewa Na Karbi Musulunci Ne Saboda Nagartar Musulunci Da Na Gani A Wajen Wasu Kwastomomina Hausawa Katsinawa. Kuma Na ZaÉ“i Sunan Aisha Saboda Sunan Yana Yi Min DaÉ—i”, In ji Misis Helen Wadda Ta Karbi Musulunci Da Yammacin Yau Lahadi
Daga karshe muna rowan allah ya kara daukaka musulunci da musulmai ya kaskantar da kafirci da kafirai baki daya hakika wannan wani babban al’amarine na farin ciki ga dukkan musulmi mai kishin musulunci da musulmai baki daya muna fatan allah ya karo dubu da ita su musulunta ameen ya allah.
Daga Mustapha Muhammad dan asalin jihar katsina state ma’aikacin gwamnatin jihar mai gudanar da aikin shi karkashin ofishin hisba na jihar katsina kuma daya daga cikin members, na kula da jagorancin al’ummar yankin na fadin jihar ta katsina dake arewa maso gabashin nigeria.