Wani matashi kwanakin baya da labarin shi ya karade shafukan sada zumunta na social media, biyo bayan wallafa wani labari dangane da cewa yayi tattaki a keke har zuwa kasar Saudiyya kuma ya dawo lafiya.
A jiya ne matashin ya kara wallafa wani labari dangane da bayyana ra’ayin tafiyar da zai karayi izuwa birnin abuja domin kaiwa maigidan shi, ziyara sabon shugaban kasa wato Alhaji bola ahmed tinubu domin taya shi murnan zaben da yayi nasara.
Mutumin Da Ya Je Saudiyya Akan Keke Daga Garin Jos, Ya Sake Yin Tattakin A Keke Zuwa Abuja Domin Taya Tinubu Murnar Cin Zaben da yayi na wannan shekarar ta 2023 a kasar mu nigeria.
Rahotanni sun nuna cewa bayan isowarsa Abuja, an hada shi da wasu daga cikin mutanan sabon shugaban kasar Alhaji Bola Ahmed Tinubu, inda za suyi masa iso zuwa ga zababben shugaban kasan.
Hakika wannan mutumin ya kasance mai kwazo da kuma jajircewa wurin kaiwa ziyara ga sabon shugaban kasar na nigeria, badan kudi ko wani abin duniya ba da zaije neman wurin sabon shugaban kasar ba.