Minister kula da walwala da kuma taimakon al’umma a nigeria sadiya umar faruq ta bayyana cewa daga lokacin hawan su, mulkin nigeria kawo yanzu sun fitar da talakawa sama da mutum million (100) daga talauci a nigeria.
Sadiya umar faruq ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai na gidan jaridar BBC Hausa dake nigeria yayin zantawa ta karshe da zatayi a cikin mulkin da suka gudanar daga lokacin da suka karbi mulkin kasar nan kawo yanzu.
Hakika talakawan nigeria basu da bakin godiya a garemu domin irin adalcin da mukayi musu na fitar dasu daga talauci da mukayi a cikin wannan kasa tamu ta nigeria inji minister sadiya umar faruq din data bayyana hakan.
Saidai da yawa al’ummar nigeria suna ta tofa albarkacin bakin su, dangane da wannan batu bayan da tayi wannan furuci akan talakawan kasar nan, wanda wasu da yawa suna ganin babu adalci da wannan mata tayi akan al’ummar kasar mu nigeria.