Muhimmancin daddawa a jikin dan adam

Daddawa a Hausar mafi yawan jahohinmu na Arewacin Nijeriya, a Sokoto suna kiran ta da suna Daudawa. A harshen Englishi ana kiran ta da locust bean cake.

Kabilar Tibi suna kiranta da suna ‘Nune, Yoruba suna kiranta da ‘iyere’, su kuma kanuri suna yi mata suna da ‘runo’.

A harshen Igbo suna ce mata ‘Ogiri’ su kuma fulani suna kiranta da ‘ makari’.

Wadannan harsuna suke nuna cewa kusan kowace kabila a Nijeriya tana amfani da Daddawa wadda a mafi yawa ake yi da diyan dorowa.

Ko a baya ga Nijeriya, kasashe masu yawan gaske a Afirika suna da wannan itaciyar da ake sarrafa diyanta a maida su daddawa, kamar Sudan, Sierra Leon, CotediCboire , Senegal, Chad, Gambia, Cameroon, Zaire, Guinea bissau, Ghana, Mali, Niger republic, Burkinafaso, Togo, Uganda da kuma Benin republic.

A mafi yawa mun dauka cewa talaka marasa karfi kawai ke amfani da daddawa, ba tare da la’akari da amfanin ta galafiyar jikinmu ba,

Wani zai gommace ka ba shi naman naira dari biyu da ka bashi daddawa ta naira dari biyar, bai san yana hanawa jikinsa wasu muhimman sinadarai masu amfanar jikinsa bane

Wasu sun dauki daddawa kayan wari wadanda kayan gyaran abincin talaka ne kawai.

Abubuwa da dama masu amfanar jikinmu mukan yi watsi da su kodan rashin sani, ko kuma don rashin dandanonsu a baki ko rashin kamshin da suke da shi.

A hakika daddawa tana da matukar amfani kwarai da gaske a jikin Dan adam

Ga kadan daga cikin muhimman abubuwan dake kumshe a cikin Daddawa.

-Kashi 29 na lipid.

-Kashi 35 na protein.

-kashi 16 na carbohydrate.

-fat. -calcium. -Ash. -fibre.

-Carotenoids(Bitamin A. -Ascorbic acid (bit.C).

Daddawa tana dai-daita sinadiran cholesterol.

Daddawa tana taimakawa dan inganta lafiyar idanu.

Daddawa tana taimakawa dan narkar da abinci.

Daddawa na maganin bugun jini da yawan haihawar jinin

Wannan ya biyo bayan binciken da wasu masana su ka yi wanda aka wallafa a mujallar nan mai suna ‘science Journal dake a birnin Dakar, na Senegal.

Inda suka baiwa beraye don su ga ko tana dai-daita gudanan jinni a jiki.

Daga karshe dai sakamakon ya nuna cewa yawan amfani da daddawa yana taimakawa don rage bugun jini a jikin Dan adam

Ana amfani da ganyen dorowa bayan an tafasa shi sai a yi wanka da ruwan yana magance zazzabi da yawan kasala da ciwon jiki.

Tana dai-daita aikin abinci a cikin cikin mutum

Tana fada da kwayoyin cuta.

Tana dauke da sinadiran tannis wadanda ke da amfani wajen tsaida gudawa.

Sassaken itaciyar na maganin gyambon kafa kona fata a jiki. Har ila yau ana amfani da sassaken a maida shi gari a dunga amfani da shi dan maganin kuturta.

A kasar cotediboire suna amfani da ganye da sassaken dorowa dan maganin zafin jiki na zazzabi da kuma wasu magunnan iska.

Idan kana fama da yawan tashin zuciya a duk sanda ka ci abinci to a dunga amfani da daddawa ka ga ikon allah

Idan kana fama da karamcin gani to ka rinka shan miyar daudawa.
Ganinka zai inganta. Daddawa tana inganta lafiyar ciki.

Tana gyara yawu ta yanda za ka rinka cin abinci kana jin dandanonsa.

Tana taimakawa garkuwar jiki dan samun damar yakar kwayoyin cuta a sanadinta na samuwar bitamin C.

Daddawa tafi aiki a cikin miyar kuka musamman idan an saka nama.

Amfani da miyar kukar da aka girka da daddawa tare da tafarnuwa na magance basir da cuttukan ciki da da sauran kwayoyin cuta.

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *