Muhimmanci da tasiri da Kuma amfanin jigida a kugun mace.
Jigida kamar yadda akafi saninta a hausance wata damarace d Mata suke daurawa a kugunsu.
Shidai jigida a tun dori ana yinsane da dutse na sakiya gamasu Hali,su Kuma talakawa ana musu tasu jigidan ne da wani roba Mai dauke d launuka daban daban domin karawa abun kyau d armashi a idanuwan Mai kallo.
Larabawa da indiyawa sune sukafi amfani da jigida tun fil, azal kamar yadda bincike ya nuna. Hakan kuwa baya rasa nasaba da yanayin yadda suke rawar Al,adarsu inda suke kada da girgiza kugunsu jigida na Aman sauti Yana hawa Yana sauka.
Saidai a baya kabilu da damar gaske na Africa suna amfani d jigida sosai fiye da yadda Larabawa da indiyawa sukeyi ganin yadda su bakaken Africa suka maida jigida cikin wani jerin al, adunsu da Kuma wani camfe camfe irin Nasu.
Wasu daga cikin camfin da aka yima jigida a africa shine, Yana taimakawa Mata masu ciki sauki wajan haihuwa, hakanan Kuma budurwa da take Sanya jigida tafi saurin sa, ar aure da wuri, haka Kuma duk macan da take Sanya jigida aljannu ko wani abubuwa na sammu bazai Kamata ba a camfi nawasu kamilun Africa.
Shidai jigida irinna da bahakanan kawai ake sakata ba, domin shahararru Kuma jarumai awancan lokacin suke yinta Don hakane take d tasiri da Kuma tsada gamasu saye.
Saidai abaya akwai jigida na “Yan Mata akwai na matan aure da Kuma na tsofaffi, Kuma a wannan lokacin babu matsala ko Kuma wani gani_gani da ake yima macen d aka ganta sanye d jigida domin abune da aka daukana al, adah Mai makon Ado ko Kiran maza da wasu ke ganin matan yanzu sukeyi da jigida ba.
Yanzu Dai Sanya jigida ga Mata ya bunkasa ya fadada Har cikin turai. Matan turawa kamar yadda bincike ya tabbatar Kashi 60 cikin 100 suna sawa.
Saidai a wannan zamanin da muke ciki Sanya jigida ga Mata yazama abun Ado ne, ba domin dalilai irin na camfi da muka ambata abaya da mutanan baya suke yiba,duk dayake ana samun kadan daga cikin matan kauyawa masu saka jigida da manufa na camfi
Shima Dai kamar irin na Dane a wannan zamanin anayin jigida ne da wasu duwatsu kalli d wasu robobi masu sheki wadanda nauyinsu baikai irin na zamanin baya ba.
Kara ko sautin da yake fitowa daga jigida a lokacin wasannin motsa Sha, awa da Kuma lokacin gudanar d jima, i abune dake himmata maza yake Kuma Kara masu kuzari d azama.
Saidai duk da wadannan tasiri, da mahimmanci da amfanun da jigida take dasu baduka Mata bane Suke sanyawa ba, Hakama maza da dama basu son ganin mace da jigida. Wasu mutane sun riga sun kudura cewa duk mace ko budurwa da akaga tanasa jigida ko akaji sautinta atare da ita suna daukar irin wadannan matan mazinata ne.
Shidai shan koko bukatar rai. Abincin wani gubar wani
Babban amfanun da jigida yake yima Mata kamar yadda bincike ya tabbatar a wannan lokacin shine, Yana karawa mace fadin kuguta ga irin matan Nan dake da karancinsa.
Maza da dama da, aka zanta dasu sun nuna Sha, awarsu naganin matansu na aure suna sake jigida domin Yana Kara masu kyau, musamman Idan mace tana sanye da kayan da zasu bayyanata.
Har ila yau cikin amfanin da jigida ke dashi Yana motsa Sha, awan maza ayayin d sukaji sautinta ko suka hango shatinta