MEYASA MAFI YAWANCIN MATA BASA IYA BAMBANCE WA TSAKANIN SO NA SOYAYYA, DA SO NA MU’AMALA?

Yawancin mata sun fi ba ma so na soyayya muhimmanci fiye da so na mu’amala saboda sun ɗauka kawai faɗin kalmar ina sonki, ko ina sonka shi ne yake nu na haƙiƙanin ana son juna.

Ki mu’amalanci wanda kike so, ki ba shi lokaci ki fahimce shi ta nan za ki ga ne ko wane iri ne shi ta nan za ki koyi yadda za ki zauna dashi domin kin ri ga kin fahimce shi mutum ne mai:

  • Sauƙin hali
  • Wuyar sha’ani
  • Saurin fushi
  • Haƙuri
  • Mai kishi

Wane irin abinci yafi so, da wanda ba ya so

Da abubuwan da ranshi ke so da waɗanda ba ya so

Kinga Idan kika mu’amalance shi ki ka gane shi ko da kun yi aure baki da damuwa domin kin riga kin fahimce waye mijinki.

Irin wannan ne saboda sanin halin miji sai ka ji ana cewa mace ta mallake mijin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *