Ita cutar ciwon sanyi wata kwayar cuta CE ta bacteria ke haddasata, wacce turawa suke kiranta da suna (Neisseria Ghonorea), sannan ita wannan cuta tana rayuwa ne a waje me damshi a jikin dan-adam mace ko namiji. Ba wai don an kirata da ciwon sanyi hakan yana nufin sanyi na yanayin duniya ke kawota ba! Ah a an kirata da ciwon sanyine sbd ita cutar gun jiqa/damshi take zama a jikin DAN-ADAM. Misalin inda cutar take zama:
- Farji=farjin mace wani kogo ne da baya rabuwa da jiqa/damshi, shiyasa da zarar cutar ta shiga ciki sai tayi wahalar fita ko warkewa.
- Mahaifa/mafi tsara=duka wadannan wurare basa rabuwa da damshi.
ALAMOMIN CIWON SANYI (INFECTION)
Manya-manyan halamominsa sun hada da;
- Jin ciwo ko zafi yayin fitsari
- Fitar farin ruwa kamar maniyyi ga namiji ga mata me kauri kamar koko, ko kamu, me wari ko me qarni ko marar ko daya daga cikin biyu. Turawa na kiransa da (GLEET).
- Qaiqayin farji ko qurarraji, ko rajewarsa, ko jin zafinsa musamman lokacin jima’i
- Kumburin “ya” yan marena ga maza
- Rashin jin cikakkiyar gamsuwa lokacin jima’i.
Saidai wasu bata nuna musu da kowacce irin alama, sannan baza a iya gane cewa tana da ita ba ko bata da ita ba, saidai in an je asibiti an yi gwaji a kan hakan. Sannan ita wannan wacce bata nuna alama tafi bada matsala sosai musamman in ta Dade a jiki ba a ankare ba.
Allah ya kyauta