Ba zan kara aske gemu naba, saboda inajin dadinsa, cewar matashiya, wadda allah ya baiwa baiwar gemu kamar na namiji yar asalin arewacin nigeria.
Wata baiwar allah mai suna hajiya ummita ta wallafa wani labari dangane da yadda jama’a suke damunta cewa tana aske gemun ta domin banbanta kanta da maza saboda ita mace ce.
Ummita ta bayyana cewa a lokutan baya da suka gabata ta kasance tana aske gemun nata amma maimakon ya daina fitowa saima taga kawai kara karuwa yakeyi alhalin ita kuma batason ya fito mata.
Sakamakon jama’a suna damunta da magana akan hakan saidai kuma daga baya data fahimci haka allah yaso ya ganta da gemunta, kawai saita yanke shawarar cewa tama daina aske gemun saboda wannan wata baiwa ce da bakowa yake da irinta ba a cikin mata.
Matar ta kara dacewa suna matukar zaman lafiya da mijinta sannan kuma mijin nata ya kasance yana matukar kaunar ta tsakanin shi, da allah gami da soyayyar gaskiya da yake mata har cikin zuciyar shi cewar matar mai gemu irin na maza.
Ummita ta kara da cewa ina kara godiya ga allah bisa wannan baiwa da yayi mini wacce ba kowa ya samu irinta ba, don haka nadaina aske gemu na har abada.