Mata Ga Wasu Abubawan Da Suka Dace Mazanku Sunayi Muku Idan Kuna Dauke Da Ciki:

Daya daga cikin lokacin da mace take bukatar kulawa matuka a rayuwarta shine a lokacin da take dauke da ciki.

Bawai sai cikin farkon haihuwa ba kamar yadda wasu mazan a lokacin ne suka fi zumudin kulawa da matansu, a duk lokacin da matarka tayi ciki wannan kulawar dai take bukata kamar kowani lokaci.

Ga wasu abubuwan da ya kamata maza su rika yiwa matansu a lokacin da suke dauke da ciki.

Tayata Aiyukan Gida-Mata suna son suka mazansu na taimakamusu a gudanar da wasu aiyukan gida musamman a lokacinda suke da juna biyu. Hakan ba karamin farin ciki yake sakasu ba.

Koda kuna da manyan yara ko masu muku aiyuka a gida, akwai wasu aiyuka na musamman da matan suke yi da kansu, irin wadannan aiyukan mata masu dauke da ciki suna son ganin mazansu na taimaka musu gudanar da irin wadannan aiyukan.

Yi Mata Tausa-Ita mace mai ciki koda bata yi aikin komai ba a kowani lokaci a gajiye take. Don haka take so naji an yi mata tausa domin dandanne mata jikinta musamman ma tafukan kafafuwanta dana hannayenta. Babu kuma wanda zata so yayi mata wannan tausar irin mijinta.

Yawan Kiranta- Idan ka bar gida yana da kyau ka yawaita kiranta kana jin yadda take da kuma abunda take bukata.
Irin wannan kulawar duk mace na bukatarsa musamman ma a irin wannan lokacin na musamman tana dauke da cikin danku ko ‘yar ku.

Hakuri Da Ita- Idan mace nada ciki wata a wannan lokacin take daura tsana ga mijinta. Tana ma iya cewa mijinta yana wari bata son ya kusance ta.
Mata masu ciki sukan bijiro da wasu halaye da daban a lokacin da suke dauke da ciki da ba a sansu da irin wadannan hakayen ba kamin lokacin. Don haka yake da kyau maza su zama suna iya yin hakuri da duk wasu sabbin dabi’un da suka ga matansu sun fito da su a lokacin da suke dauke da ciki.

Yi Kokarin Fatanta Mata Rai- Kayi kokarin ganin a kowani lokaci matarka tana cikin farin ciki musamman ma a lokacin nan datake dauke da ci.
Samun farin cikinta yakan taimakawa lafiyan abunda take dauke danshi ita ma kanta.
A lokacin da mace take dauke da cikin yanada kyau maigida ya koyi barkwanci na yadda zai rika sanya matarsa fara’a da farin ciki har Allah Ya sauketa lafiya.

Ka Samamata Abubuwan Kwalama- Ba komai mata suke iya ci ba a lokacinda suke dauke da ciki. Kayi kokarin ganin ka samarmata duk wani abunda take kwadayi dai-dai karfin samunku a duk lokacin da ta bukaci hakan.
Akwai lokacinda ma zatace ita girkin da ka dafa take son taci, idan har ka iya sai ka daure ka girls mata.

Kyututtuka- Kafi kowa sannin abunda matarka take so, ka yawaita yi mata kyauta na bazata na abubuwan da kananan tanaso. Hakan yana kara sata natsuwa da kwanciyar hankali.

Kanuna Mata Kaunar Abunda Take Dauke Dashi- Ka fita alfahari da abunda ke cikin cikinta. Ka nuna mata yadda kake son abunda zata haifa fiye da abunda kuka haifa a baya.

Mata gaba daya sauyawa suke yi a dabi’a dama kamanni a wannan lokacinda suke dauke da juna biyu. Wannan yasa suke bukatan kulawa na musamman fiye da lokacin da kayi dokinta tana amarci.
Allah Ya sauki mata masu juna biyu lafiya. Wadanda Allah Bai basu haihuwa ba, Allah Ya kawo musu haihuwan idan shine mafi alheri a rayuwarsu.

Mu kuma da muka haifa Allah Ya shiryar da abunda muka haifa dama wadanda zamu haifa nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *