Nonon rakumi shine Nono mafi amfani aduniya. Yafi kowanne nonon dabbobi amfani ajikin ‘Dan Adam.
- Yafi kowanne nono yin kama da nonon ‘Dan Adam.
- Yana kunshe da sinadarin Calcium.
- Vitamin B, da C din da suke cikinsa sun ninka na nonon saniya fiye da sau uku.
- Sinadarin IRON din da yake cikinsa ya ninka na nonon saniya fiye da sau 10.
- Akwai Sinadarin INSULIN mai yawa acikinsa.
- Yana maganin ciwon Sugar (Diabates).
- Yana maganin ciwon Kumburin hanta. (Heppatittis).
- Yana maganin ciwon zuciya (heart failure).
- Yana Qarfafa garkuwar jikin ‘Dan Adam ta wajen yaki da cututtuka.
- Mai da kitsen da yake cikinsa ba ya chutar da lafiyar dan Adam.