Saidai Rubutun nawa dole zai danyi tsayi, a karba da hakuri.
Gemun masara shine wani abu mai kada da zare ko gashi da ake samu a jikin masara danya. An dade ana amfani dashi wurin magungunan gargajiya a karnoni da dama da suka wuce. Hakan yasa masu bincike na kimiyya da fasaha suka dukufa domin samo dalilan magungunan da yakeyi tare da tabbatar da gaskiyar tasirinsa wurin magance cutukan da ake amfani da shi wurin magacesu.
Gemun masara yana dauke da sinadaran fiber, antioxidants (flavonoids), vitamins, minerals, carbohydrates, da kuma proteins.
Bincike na kimiyya da fasaha da tarihin magungunan gargajiya sunyi tarayya a cikin tabbatar da tasirin wannan gemu na masara wurin magance cutuka kamar haka:
- Yin shayinshi tare da turmeric (kurkur) yana magance matsalar nan ta inflammation (kumburi a matakin kwayoyin halitta). Shi inflammation kusan zamu iya cewa shine mafarin kusan dukkan matsalolin jiki kamar ciwon ulcer, ciwon gabobi, hawan jini, cutar sugar, basir, fibroid, zafin fitsari, da sauransu. Ko buguwa mutum yayi, ko ciwon kai ko kuma wani wuri na jikinsa ya rike yake masa ciwo, inflammation shine yake haddasa ciwon da kuma dadewar ciwon. Abinda yake faruwa shine, yayinda wani abu ya faru ko buguwa ko kuma garkuwar jikin mutum yakai hari wurin ba a daidai ba akan samu samuwar wasu sinadarai da ake kira inflammation mediating chemicals, wanda su kuma suna motsa pain sensitive receptors suyita aika sakon zafi zuwa kwakwalwa har sai lokacin da aka daina samar da inflammation mediating chemicals din. Shiyasa duk wani magani da yake amsa sunan pain killer yana magance inflammation ne, shiyasa ma sunansu ya zama Nonm-steroidal Antiinflammatory Drugs (NSAIDs). To shi gemun masara yana da sinadaran da suke magance wannan matsala ta inflammation.
- A wani bincike da wasu masu bincike sukayi a university of Akron, United State of America da kuma wani asibiti mai suna Essraa a Jordan sun tabbatar da cewa ciwon koda ko da takai ga yin dialysis ko kuma an fara tunanin dashen koda, matukar aka samu gemun masara da garin habba (blackseed) da busasshen nonon rakumi aka tafasa aka barshi ya huce mara lafiyan yake sha, zai warware. Wannan hadin an jima ana amfani da shi tun kafin wannan binciken nasu.
- Cancer din mama na daya daga cikin matsalolin da suka addabi mata a duniya musamman kasashe masu tasowa, binciken da wasu masana sukayi a Jami’ar King Sa’ud dake Riyadh, Saudi Arabia, sun tabbatar da cewa shan ruwan da akan jika gemun masara yana hana ci gaba da girman kwayoyin halittar cancer (cancer cells) sannan yana sanyasu sum utu da kansu (apoptosis). Lizimtar shan ruwan yana tafiyar da cancer din maman. Dama dai an dade ana amfani shi a gargajiyance wurin magance cutukan jeji.
- Ko da cutar Hepatitis tayi chronic a samu tafarnuwa da gemun masara da busasshen namijin goro a dakasu sannan a saka Baking soda (sodium Bicarbonate) a dunga zubawa a ruwan dumi ana saka mazarkwaila ana sha, tabbas zaa rabu da cutar.
- Wani bincike da wasu masana sukayi a wani asibiti mai suna Hospital of Chengdu dake cikin University of Traditional medicine dake china sun gwada a kimiyyance tasirin gemun masara wurin magance hawan jinni, kuma sakamakon bincikensu ya tabbatar yana da tasirin gaske wurin magance hawan jinni. Haka kuma ciwon zuciya (heart failure) yana taimakawa wurin dawoda ayyukan zuciya yadda suke ainihi.
- Ciwon kirji wanda yake sanya nauyin numfashi, gemun masara magani ne sadidan da yake warkar dashi. An dade ana amfani dashi a gargajiyance wurin magance matsalar, wanda yanzu kuma binciken kimiyya da fasaha ya tabbatar da tasirinsa wurin magance ciwon kirji, musamman na ‘’Angina’’.
- Gemun masara yana magance matsalar nan ta ido da ake kira Glaucoma da sauran rukunonin cutukan da suka shafi ido har wadanda sukan iya haddasa makanta ma. Bincike a wurare daban-daban na duniya sun tabbatar da haka.
- Masu fama da depression ku dunga yin shayin gemun masara da na’a-na’a ko kanunfari ko charmomile zakuga ikon Allah, damuwar zata ragu sannan dukkan alamomin da depression ya haddasa zasu tafi.
- Masu fama da zafin fitsari suma ga magani sadidan kawai ku tafasashi kusa zuma, a sakanni zai tafiyar da zafin.
- Binciken da aka yiyyi kwanakinnan a wurare daban-daban na bincike sun tabbatar da cewa gemun masara yana hana faruwar cutar Suga (Diabetes) sannan kuma yana taimakawa wadanda suka kamu wurin sassaita adadin sugan da yake kewayawa a cikin jinni (Blood Glucose level), wanda hakan yana hana faruwar zafin tafin kafa da yake zuwarwa masu fama da suga, sannan yana hana faruwar fashewar wani sashi na jikin mai cutar suga bugu da kari yana sanya warkewar wurin idan ya faru.
- Kasancewar da yawa masana suna ganin alakar fitsarin kwance da sakonnin da suke kaikawo daga urinary bladder zuwa kwakwalwa, wasu masana na ganin cewa yin amfani da jikon gemun masara yana taimakawa wurin hana fitsarin kwance.
Har yanzu ana kan yin bincike game da gemun masara, domin irin alkhairan da duniyar magani ta hango game da wannan zare mai sirri suna da mugun yawa. Kaidai naka dan uwa kayi kokari ku saba da gemun masara koda baka da wata matsala domin yana hana afkuwar manyan cutuka kuma yana kara kaimin garkuwar jiki.
ALLAH yasa mu dace.