MAGANIN WARIN BAKI DA DATTIN HAKORA

Sakamakon ciye ciye na yau da kullum da mukeyi.a ci wannan a sha wannan,hakora kan yi dattin. Sakamakon haka na haifar da wasu cutuka a cikin baki oral infections saboda taruwar kazamta a cikin bakin.

Haka kuma zaka tarar baki na wari,ta yanda magana a cikin jama’a zai maka wuya,ko kuma sumbatar matarka ko mijinki zai zamo wani abin kyama da qazanta.

To idan ka tsinci kanka da Wannan matsalar ga hanya ingantatta mafi sauki da zaka bi ka tsabtace bakinka da hakoranka. Zasu daina wari kuma hakoranka zasu yi haske.

a nemi garin citta karamin cokali daya da baking powder wacce masu yin bread ke amfani da ita rabin cokali

Sai ka gauraya sai ka matse lemun tsami daya a ciki sai ka saka a brush ka goge hakoranka da kyau sannan ka kurkure bakinka da ruwa ka zubar.

Idan ka fake yin hakan zaka ga hakoranka sun yi haske haka kuma bakinka zai daina wari,hakoranka zasu yi karfi su kuma kara lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *