MAGANIN ULCER SAHIHI,DA GANYEN GOBA

Duk mai fama da matsalar stomach ulcer insha Allau Wannan fa’ida zai iya jarrabawa,kuma cikin nufin Allah da yardar sa zai samu waraka.

Bayan magance ulcer kuma yana kara kare jikin mutum daga kamuwa da wasu cutuka masu karya garkuwar jiki.

ABINDA ZAA NEMA

Ganyen Goba guda 6 zuwa 10
Ruwa lita 1

Za’a samu ganyen mai kyau sai a wanke shi, sannan a jajjaga shi kadan sannan a hada da ruwan lita daya a tafasa shi har sai ruwan ya sauya kala.

Sannan a sauke a tace,idan ya huce a rika shan karamin kofi sau 3 a rana,ga babbam mutum yara daga shekara 6 zuwa 15 sau biyu ranin karamin kofi.

Mace mai ciki ma zata iya sha domin yana taimakawa sosai,haka na mace mai fama da matsalar alada ma zata iya wannan hadin.

Allah yasa mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *