MAGANIN TARI DA MURANA KANANAN YARA

A lokacin sanyi yara ƙanana suna yawan fama da yawan tari ko mura to insha Allah ga hanyar magancewa cikin sauki.

JARIRI DAN WATA 1 ZUWA 2

Idan jariri ne bai wuce wata daya zuwa biyu ba zaa samu man tafarnuwa a rika shafa masa a hancin sa da kirjin sa kullum safe da yamma, a kiyaye yi masa wanka da safe ko barin sa iska tana samun sa.

YARO DAN WATA 5 ZUWA 10

A samu man shanu a hada da man zaitun a rika shafe masa hancin sa da kirji sau 2 a rana, sannan a rika diga masa man tafarnuwa wanda aka hada da man hulba,kamar digo 5.

YARO DAN WATA 10 ZUWA SHEKARA 1

Ana samu zuma kamar chokali 5 lemon tsani karami a Raba 4 a matsa rabi akan zumar a rika bashi rabin karamin chokali 1 da safe da yamma..

Allah yasa a dace.

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *