MAGANIN TARI CIKIN SAUKI DA YARDAR ALLAH

Bisa Fara shigowar Sanyi Da Kura da akeyi Yana da kyau al’umma a dinga amfani da amawalin hanci domin Samun kariya daga Kura dake shiga hancinanmu ya wuce zuwa hunhun mu. Daga karshe kaga Tari ko Asthma ko allergies ya kama mutum.

Idan Allah yasa mutum yakamu da tarin sai ya samu wadannan kayayyaki Kamar haka:

Citta cokali 2

kajiji cokali 2

marke cokali 5

Ruba Tari a busar da ganyen shi a zuba cokali 3

Tafarnuwa cokali Daya

Kanumfari da masoro duk cokali biyu-biyu Suma.

Cinnamon cokali 2

Sai a hade waje Daya gaba daya a dinga tafasa ruwa Rabin Kofi ana zuba maganin karamin cokali Daya wato teaspoon sai asa Zuma cokali 3 adinga Sha safe dare da Yardar Allah za’a samu waraka cikin Sauki.

Masu Allergies ko Asthma suna iya tuntubarmu domin siyan nasu maganin da Baza su shiga Cikin damuwa ba a wannan Sanyin da Yardar Allah.

Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *