Wani layi-layi dake fitowa mata ajikinsu, musamman masu ƙiba.
Yakan fito a gurare kamar wajen mara, kamar ga macen data haihu,
Yakan fito a wajen gwiwar ƙafa da kafaɗar mace dssr.
Duk wacce take fama da irin wannan abin ga abinda zata nema
ALOE-VERA: Ki tatse farin ruwan aloe -vera kullum ki rinƙa shafawa a wurin idan ya bushe sosai saiki wanke da ruwan ɗumi.
Ko kuma ki ɗebi man aloe-vera chokali ɗaya ki haɗa da vitamin E oil capsule ɗaya ki rinƙa shafawa a wurin.
Da iznin ALLAH zaki nemeshi ki rasa.
Maganin wannan tabon na biyu shine:
Ki fasa ƙwai ɗaya ki cire ƙwaiduwan ƙwan, sai kiyi amfani da cokali kiyita kaɗa farin ƙwan har sai yayi kauri yayi fari tas kamar cream,
Sannan ki shafa a wurin layi-layin ki barshi ya bushe sannan ki wanke da ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu.
Da iznin ALLAH zai ɓace