MAGANIN RAGE QIBA DA TUMBI

Salam Dan Allah inaso adan fada min abubuwan dazan yi amfani dasu wajan ragi kiba da tumbi.wslm

AMSA

Ga wasu hanyoyin nan agwada da izin Allah, insha Allahu za’a samu biyan buqata._

MAGANIN RAGE QIBA

Da farko dai ki zama mai yawan motsa jikinki wajen ( training ).
Na biyu sai ki samu wadannan sirrin kina yin shayi kina sha safe da yamma.

shayi ba madara
Lipton
lemon tsami
na’a-na’a

Da farko ki tafasa shayi ba madara tare da Lipton da na’a-na’a da kayan kamshi, sai ki matsa lemon tsami a ciki ki sa sukari ki rikka sha safe da yamma tare da yawan motsa jinkinki a duk lokacin da kika sha. To insha Allah Zaki ga yadda jikinki zai komo bayan wata daya._

MAGANIN RAGE TUMBI

​ki tanadi ​lemun zaki​ da ​citta​ A tafasasu minti hudu zuwa biyar a yi shayi ban da madara A zuba ​MA UL KHAL​ cokali daya ko biyu cikin kofin shayin a sha da ganyen shayi kamar ​Lipton​ da zuma ko suga Za a yi haka sau biyu a kullum Haka kuma za ki iya amfani da ​lemun tsami​ amadadin ​MA UL KHAL​ din Bayan haka mutum ya rika motsa jiki a kai a kai Idan kina ganin cewa ba ki da lokacin motsa jiki to sai ki rika gudanar da wasu aikace aikacen gida da kan ki.​

Bayan wannan za ki iya​ ​samun ​kwayar ya yan Zogale​ a markada​ ​a hada da ruwan zafi a rika sha da safe da dare yana maganin rage kiba ko tumbi.​

hulba garin na’a-na’a garin kanun fari zuma lemon tsami farin kwalli manna’a-na’a ki hadewadannan ganye guri 1 ki tafasa ki sami farin kwalli dunqulen zaki saka a ciki, idan ya kai kamar minti 5 sa ki cire, sannan ki saka zuma a cikin ruwan sha,
ki samu man na’a-na’a rinka shafawa, tumbi ki zai ragu insha Allah idan kuma anason rage kiba ne za ‘a rinka zuba lemon tsami a ciki_

Ganyen na’a na’a kamar guda 10 zuwa 12._
kokumba guda daya dan madaidaci.Lemon tsami guda daya.

Danyar cittamarkadadde cikin karamin cokali.
Ruwa lita biyu

Yadda ake hadawa

Za’a Jika gaba daya kayan hadin a cikin ruwa da daddare ya kwana. Washe gari ayi ta shan sa a matsayin ruwa.

Ayi ta maimaita hakan har sai an samu yadda ake so.

`Allah ta’ala yasa mudace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *