MAGANIN LAULAYIN CIKIKI HADA WADANNAN
Ganyen Na’a-Na’a (Fresh ko busashe mai kyau)
Lemon tsami.
Zuma mai kyau.
Citta da Kanumfari
Adafa ganyen Na’a-Na’a kamar cokali uku acikin ruwa kofi daya. Azuba citta da kanumfari daidai misali a dafasu tare.
Idan an sauke, an tache ruwan sai a zuba zuma gwargwadon yadda ake so. Sannan a yanka lemon tsami guda biyu. amatse acikin ruwan tea din sannan a sha.
In sha Allahu za’a samu sauki. Mai Juna biyun zata samu Karfin jiki, zata dena yawan zubar da yawu (Miyau) Kuma jaririn dake cikinta zai samu kaifin basira da Hankali in shaa Allah.
Allah ya sauki dukkan masu juna biyun Musulmai Lafiya. Wadanda aka haifa kuma Allah shi raya mana