MAGANIN GAGARARREN SANYIN MARA NA MAZA DA MATA FISABILILLAH

Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.

Ga kadan daga Alamomin cutar sanyin mara.

Dauke sha’awa

Fitar farin ruwa daga gaba

Tsagewar farji

Fitar kuraje a gaban mace ko namiji

Saurin inzalii

Ciwon idanu,har yakan sa a daina gani

Fiyar kuraje a jiki ko wani sashe na jiki.

fitar kuraje a baki da makogaru .

Amma fa bacterial infection suna da yawa,amma mu masu maganin hausa duk suna daya ake kiran su dashi wato sanyin mara.

Amma a ilimin zamani na likitanci suna da sunayen su daban daban ga kadan daga cikin su

Candida

Pelvic inflammatory disease(pid)

Gonorrhea

Urinary tract infection

Chlamydia

bacterial vaginosis

Wadan nan sune kadan daga cikin su,sai dai ta hanyar alamomi kusan baa iya banbancewa domin wasu lokutan suna da makamantan alamu,saboda haka aje ga likita domin sanin kalar wanda mutum yake dauke dashi

Amma ga kowannne a cikin su ga hanyar da zaa magance shi insha Allah.

Domin magance wannan cuta.

Ganyen Garafuni (Monordica)
Kaninfari(Clove)
Tafarnuwa (Garlic)

Zaa samu ganyen Garafuni danye kamar cikin tafin hannu,ko manyan kunne guda 10.

Kaninfari chokali 1, Tafarnuwa Sili 10,zaa hade waje daya da ruwa Liter 3 zaa dafa sosai kamar minti 20.

Bayan an sauke a tace a zuba a wani mazubi me kyau a aje a fridge a rika shan kofi daya safe daya dare.

Mata da muji susha tare,amma banda mace mai ciki.

Za’a sha tsawon sati 3 insha Allah zaa samu waraka insha Allah.
🧄

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *