MAGANIN CIWON MARA’ GA NAMIJI’KO MACE

A lura wajen hada maganin kada ayi ba daidai ba

Mata Masu Fama da zafin Mara A Yayin da Al’ada Tazo Musu zasu Iya Jarrabawa kuma da yardar Allah za’a dace kuma Ayi Hamdala’

MAHADIN MAGANIN SUNE KAMAR HAKA”

Tsamiya Guda Biyu’ Ma’ana Tsamiya Sili Biyu.

Garin Habbatus-Sauda Cokali 1′ Koshiya Daya.

Ruwa Kofin Shayi Babba Guda Biyu
“Zuma pure Mai Kyau Wacca Babu Gauraye a ciki.

GA YANDA ZAKA HADA MAGANIN KO YANDA ZAKI HADA MAGANIN”

Za’a Samu Ruwan Kofin Shayi Biyu A Dorashi akan Murhu Sai a Saka Silin Tsamiya Guda biyu Sai A Saka Garin Habbatus-sauda Cokali daya koshiya daya’ Sai a zuba Acikin Ruwan’ sai a Tafasa su’ idan Sun Tafasa’ Sai a samo zuma’ Kamar Cokali biyu ko Uku’ Sai a Raba Ruwan Biyu’ zai zama kofi daya kenan’ Sai a zuba zumar cokali 2′ ko Uku A shanye’ A ajiye Daya Kofin’ idan yamma tayi’ Sai a Kara Tafasashi’ a zuba zumar Cokali 2 ko uku’ A Samu Kamar Wata Huda Anayi Insha Allah Ciwon Mara Ko Wanne Irine za’a Rabu dashi”

Abin Sadaka ayi salati ga Annabi Muhammadu S. A. W.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *