Maganin Ciwon Haƙori Sahihi

Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakaatuh, barkan mu da sake haɗuwa a wannan lokacin.. a yau In shaa Allah zanyi bayani akan yadda za’a magance matsalar ciwon haƙori duk tsananin sa In shaa Allah..

akwai hanyoyi masu yawa da Za’a iya amfani dasu, zanyi bayanin Ukku 3 daga cikin su.. sune kamar haka

asamu zuma mai kyau a dinga yin brush da ita da safe da kuma da dare., Sai a nemo Khal Tuffa wato Apple cider Ana samunsa a wurin masu Islamic Medicines, sai tun da safe Bayan anyi brush da zuma sai a zuba shi Khal tuffa ɗin a cikin ruwa masu ɗumi, wato masu zafi-zafi sai a ƙara da gishiri ɗan kaɗan a riƙa kuskure baki dashi har sau uku, da dare a maimaita hakan, a cigaba dayin haka har tsawon kamar sati ɗaya In shaa Allah za’a nemi ciwon haƙori a rasa baki ɗaya.

A samu garin Khusdil Hindi wato Sanya a riƙa gogawa akan haƙori ko dasashin da yake ciwo sai a wanke baki da ruwa masu ɗan zafi-zafi wato masu ɗumi.

A samu garin sassaƙen iccen giginya a haɗa da garin jar kanwa ana gogawa a inda yake ciwo ko asa a ruwa masu ɗumi ana kuskure baki dashi.

Idan kuma hauren yayi kogo, matuƙar kogon baiyi zurfi ba, toh sai a haɗa garin Khusdil Hindi da man habbatussauda ayi mix ɗin shi wuri ɗaya a riƙa ɗiba ana sakashi a cikin ramin kogon idan za’ayi bacci, da safe sai a wanke da ruwa masu ɗumi, in shaa Allah zai daina ciwo, kuma dasashin wurin zai riƙa cikowa har wurin ya cike baki ɗaya, AMMA idan ramin kogon yayi zurfi ƙwarai toh aje asibiti ayi ciko ko a cire shine kawai mafita… Allah yasa mudace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *