MABUDAN YAYEWAR DAMUWA GUDA 10

Sadaukarwa ga mahaifana, Allah ya isar Masu da ladan zuwa kabarinsu.

Mabudi na farko.
Karanta suratul fatiha ‘ita tana wadatar da Mara lafiya domin tana warkarwa ‘ita ruqya CE.

Mabudi na biyu.
Fadin wannan addu’a a lokacin damuwa,
الله الله ربي لا أشرك به شيئا
Manzo s.a.w yacewa ‘yarsa fadima, lokacin damuwa kice ” الله الله ربي لا أشرك به شيئا “

Mabudi na uku.
Fadin” لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين ” manzo s.a.w yace, addu’ar dan’uwana zeennun (annabi yunus) wanda yashiga damuwa bazai fadeta ba face Allah ya yaye masa.

Mabudi na hudu.
Fadin” حسبنا الله و نعم الوكيل ” qur’ani ya bamu labarin cewa lokacin da akazo don a tsorata musulmai cewa abokan gabansu sunyi musu tanadi babba don suji tsoronsu sai suka fadi wannan addu’a sai Allah ya amintar dasu sharrin abokan gabansu suka dawo cikeda ni’ima da falala babu wani abinki daya samesu.

Mabudi na biyar.
Fadin” لاحول و لا قوة إلا بالله العلي العظيم ” Allah zai yaye ma bawa damuwa dalilin fadinta, kuma ‘ita taskace daga taskokin aljanna.

Mabudi na shida.
Yawaita istigfari, manzo s.a.w yace mai yawaita istigfari Allah zai sanya masa yayewa akowace damuwa, da mafita akowane qunci yakuma azurtashi ta inda baiyi tsammani ba

Mabudi na bakwai.
Fadin wannan addu’a. Duk wanda ya lizimceta Allah zai yaye masa damuwoyi.
“لا إله إلا الله العظيم الحليم ،لا إله إلا الله رب العرش العظيم ،لا إله إلا الله رب السموات و الأرض رب العرش الكريم “

Mabudi na takwas.
Lizimci wannan addu’a manzo s.a.w yace tana yaye damuwoyi kamar yadda ta tabbata a ingantaccen hadithi.
” اللهم إني أعوذ بك من الهم و الحزن و أعوذ بك من العجز و الكسل و أعوذ بك من البخل و الجبن و أعوذ بك من غلبة الدين و قهر الرجال “

Mabudi na Tara.
Fadin wannan addu’a
“يا حي يا قيوم لا إله إلا أنت برحمتك أستغيث “
Addu’a ce ta Neman taimakon Allah da yayewar damuwoyi manzo s.a.w ya kasance yana yinta.

Mabudi na goma.
Fadin sannan addu’a, manzo s.a.w ya kasance yana fadinta idan al’amura suka tsananta gareshi.
“اللهم رحمتك أرجو فلا تكلني إلى نفسي طرفة عين و أصلح لي شأني كله لا إله إلا أنت “

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *