LURA SOSAI DA RUWAN DA KE FITA AGABAN MACE

LURA SOSAI DA RUWAN DA KE FITA AGABAN MACE

kamar yanda kowa yasani gaban mace baya rabuwa da jika ko na ni ima ko kuma na cuta ya danganta da irin ruwan
idan akace farin ruwa ana nufin fari kal me kamar ruwan famfo shine yake zama na ni ima kuma yanada yauki sannan yanada dandano wani kamar gishiri ya danganta da irin abunda mace kesha
saidai mata da yawa farkon saduwa akwai wani farin ruwa me kamar nono dan kadan yana fitowa wannan wani ruwane wanda ba kowacce mace
ke samuba domin da yawa mace daga ta fara haifuwa shikenan kuma wannan ruwane na musamman farar mace
wani ruwan kuma yauki zakaga yanayi kuma haka kawai mace ko zance tayi da namiji zataganshi kuma me irin wannan ruwan bata taba bushewar gaba kuma daban take acikin mata
shikuma ruwa na cuta haka kawai yake zuwa agaban mace kuma bayan farine me kamar majina zakaganshi guda guda wani kuma kamar zare zare kuma ruwan yana iya canja kala daban daban wani yakoma Green wani brown kuma sauda dama warinsa yana zama kamar na danye kifi akwai kuma me warin danyen kwai
wani ruwan kuma kamar mace me ciki tana yawan ganinsa musamman bayan gama saduwa ko kuma bayan ta gama fitsari wannan shikuma dattine na mahaifa shima ba matsala bane
dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanada dashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata hudune agida aka samu daya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar wato kamar sabulai da ruwan magarya da amfanida gishiri da sauransu
HANYOYIN KARIN NI.IMA

 
wannan sassaken baure zaki samu ki zuba masa ruwa ki dora akan wuta idan ya tafasa zakiga ruwan ya canja kala
saiki sauke sannan ki tace ruwan dama kin daka kanun fari saiki zuba garin sannan ki zuba zuma kadan saiki saka bazar kwaila sannan ki mayar dashi kan wuta idan ya tafasa zakiji yana kamshi saiki saukeshi sannan ki ajiyeshi kina shansa sau biyu a rana
sai kuma wanda akeyi da kwakwa kawai kisamu aya danya sai dabino ki cire kwallon da danyen zogale da kwakwa da kankana da cukuw sai mazar kwaila
ki markadasu ki tace ruwan sannan kidauko nonon rakumi ki zuba ki gauraya ki wuni kinasha zakiga wani ruwa me maiko yana kamshi ni ima kenan
 
wannan kuma ganyen zogale Zaki dafa bayan ya dafu saiki tace ruwan kana ki yanyanka cocumber aciki ki zuba aya da farin goro ki markadasu dukkansu saiki tace ruwan sannan ki zuba madara peak ko luna kisha saidai kamar irin wannan yana saka wasu matan gudawa saboda wannan ruwan zogalen amma idan dama kinashan zogale
kada kibar wannan hadin
 
Goron tula akwai wanda don amare yake hasalima ana fada masa goron amare wato wanda yake da danko sosai da alamun gashi ajikinsa ki jarraba cinsa kamar goma yayi sama kwana5 kafin aurenki zakisha mamaki
GUMBAR KANKANA

koda yake itama gumbar kankana ana hadata da ridi kamar yanda akeyin sauran gumba amma idan kika hadata da gero tafi sauri saukarwa mace ni ima kamar yanda a wannan makon muka jarrabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *