Kun san dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu

?

Shanyewar ƙafa matsala ce da ke faruwa sakamakon lahani ga jijiyar laka da ake kira da ‘sciatic nerve’ wace ke kai saƙonni zuwa wasu tsokokin ƙafa.

Wannan jijiyar laka ta fito daga laka ne sai ta biyo ta cikin ƙashin ƙugu sannan ta ratso ta cikin tsokokin ɗuwawu zuwa ƙafa har tafin sawu.

Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar lakar yayin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya tunzira jijiyar lakar, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar lakar wanda hakan na iya danne ko shaƙe ta har aikinta ya samu cikas.

Waɗanda suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da

Wanda bai bayar da haɗin kai ba yayin yin allurar, musamman ƙananan yara da ma manyan masu tsoron allura.

Mai rama sosai.

Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.

Da kuma wanda tsautsayi ya faɗa wa.

Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukan rassan jijiyar lakar a ƙafa nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haɗa da

Matsanancin ciwo

Sagewa

Shanyewar tafin sawu

Rauni ko rashin ƙwarin ƙafa

Rashin ji a fata idan aka taɓa

Wahalar tafiya: ɗingishi, jan ƙafa da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami’in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa sumul kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya nakasa ƙafar.

Game da shanyewar ƙafa likitocin fisiyo Physiotherapists ne ke amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiyar lakar da tsokokin ƙafar ƙaimi har aikinsu ya dawo yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *