KU YIN GUJI KARYA A SOYAYYAH

  1. Ba’a soyayyah mutum daya dole ne mutum biyu,sannan kowa yana son kulawa daga dan uwan sa, mutum daya kan iya wargaza wannan soyayyar da kuke yiwa junan ku, musamman idan aka saka Rashin gaskiya a cikin sa.
  2. KARYA : babban jigo ne dake tarwatsa soyayyah a tsakanin masoya,idan daya yayiwa Dan ‘uwansa karya mace ko Namiji,duk randa asirin daya ya tuno sai kuma a daina ganin mutunci daya.
  3. Idan za’a kwatatan gaskiya a mu’amala ku da kanku,zaku cimma nasaran abinda kuke son isar wa,amma idan aka canja alakar zuwa wata bangaren daban kuma akwai matsala babba ta bangaren nan.
  4. Da yawa wasu matan sun fi son mazan yan Karya,wanda kuma hakan babban laifin ta bangaren su ne,yayin da wasu kanyi amfani da wannan son karyan nata, su mata karya,duk mai hakan idan an mata karya ita ce sanadin hakan.
  5. Idan har ana son gina soyayyah to a guji karya da Rashin gaskiya,domin Abu ce mai muni kuma mai zubar da kimar Dan Adam a tsakanin ku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *