Babu Wanda Ya Baiwa Rarara Gida Ko Mota, Kuma Ni Ma Babu Wanda Ya Bamu Komai Akan Asarar Da Mukayi Inji Baban Chinedu daya daga cikin shahararrun mawakan jam’iyyar (APC) a nigeria mazauna jihar kano.
Mun samu wannan labarin daga bakin mai yada labarai na shahararren mawakin (APC) Alhaji dauda kahutu rarara mai suna dan katsina ya shaidawa manema labarai cewa maganar da ake yadawa akan cewa an baiwa mai gidan shi motoci da kuma gidaje ba gaskiya bane wannan magana.
Daga bangaren mawaki Baban Chnedu shima ya ƙara da cewa maganar baiwa Rarara gida da mota kamar yadda wasu ƙafofin sadarwa suka yaɗa duk ƙarya ne, kuma ni ma babu wanda ya bani koda kwano akan abinda ya faru da mu.
Yakamata al’umma su daina yarda da irin maganganu na ‘yan social media domin haka kawai mutum zai kirkiri labari na kanzon kurege yana yadawa al’umma musamman akan irin wadannan abubuwa da suke faruwa damu a cikin wannan kwanaki.
Baban Chinedu ya ci gaba da cews “Bana tunanin akwai É—an siyasar da zai iya biyan Rarara asarar kuÉ—in da ya yi lokaci É—aya, akwai su, amma yin hakan ne abu mai wahala, domin yayi asara sosai, kuma nima nayi asara sosai saidai allah ya saka mana.