kalolin maganin infection

Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewa ko budewa da kwailewa da rashin sha’awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi wanda wannan gida na kowace cuta da maganinta ya binciko muku

Ga abubuwan da za a nema

A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya.
Yana maganin budewa da kaikayi.

A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa,
Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.
Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha.
Yana magance matsalar ruwan infection.
.
A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma.
Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba
.
A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha.
Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.

A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi.
Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni’ima.

A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki.
Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta.
Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna.
Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa
.
A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su tayi Yaji ta dinga cin abinci da shi.

Yana saukar da ni’ima da magance duk
matasalolin sanyi cikin ikon allah

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *