KADAN DAGA CIKIN AMFANIN BISHIYAR TUMFAFIYA

Sharadin Shine Ayi Sharing Domin Yan uwa su Amfana

Saiwar tumfafiya tana cutarwa kamar (poison) ce dan haka kada a kuskura a sha,yanda ake sarrafata dan magani da ita baya da alaqa da maganin da za a jiqa a sha a ruwa ko ga wani abin sha.
Ana amfani da ita ga wanda maciji ya ciza

Ana amfani da 6awon tumfafiya ko itatuwan waton stems a turance kenan dan maganin cutar kuturta
(leprosy).
za’a dake itatuwan a nemi man kade a kwa6a sai a shafa a inda cutarta ta bayyana.

Ana cin qwallon dake a cikin furen tumfafiya.Idan aka bude fulawar za’a ga wannan dan kwallon a cikin furen tumfafiya to shi za’a ci ba dukkanin flower ba.
yana maganin kamin mugu waton mayu kenan.Wallahi basa qaunar ruhi da jinin mai cin furen tumfafiya.Idan zaku lura zaku ga akwai wata fara da ake samu ga tumfafiya kadai mai launin kore,ita wannan farar bata da abincin da ya wuce wannan flower dake a tumfafiya.Ita ma magani ce sosai na karya sihirin maye da maitarsa.

Ana gauraya 6awon bishiyar tumfafiya da garin habbat sai a turare ko wane lungu ko daki,ko gida ko duk wani waje da ake bukata.Wannan na korar baqaqen iskoki da miyagun qwari kamar macizzai da makamantansu.

Ana gauraya garin ganyen tumfafiya dana lalle a kwa6a a shafa a inda ciwo yake.Yana maganin cutukan cin ruwa,tsagewar yatsa,ciwon yatsa na dan kakkarai.

Ana diga madarar tumfafiya wacce idan aka 6allo ganyenta za a ga madarar tana zubowa.Za’a karkare makero da dutse sai ya karkaru sai a diga a saman makeron,a fake yin haka a duk kwana biyu.

Maccen da take mafarkin iska yana zomata yana saduwa da ita ta nemi saiwar tumfafiya da kunnen gamji da garin habba ta tirare gabanta dasu.Amma kuma da sharadi idan akwai ciwon mara ko yankewar jini,ko shigar ciki,ko macen da ta haihu ko take cikin jinin al’ada sai ta nemi karin bayani.

Mai tarin fuka na asthma, ya nemi 6awon tumfafiya ya shanya su bushe ya cinna masu wuta yayi tirare.

Tsutsar ciki – A nemi furen ayi blending a tafasa a tace ruwan a tarfa Zuma kadan a sha.

Basir mai tsiron da ya fito a dubura kuma yaqi komawa yake ta zubarda jini a nemi ganyen tumfafiya kwara biyu ko uku a kara a wuta su dan yi zafi kadan sai a shafa man Vaseline a saman ganyen a danne duburar kan inda basir din yake zai koma nan take.

Ciwon jiki na shawara ka tafasa ganyen da shi da fatar ayaba ka tsaye ruwan kayi wanka dasu safe da yamma.

Cutukan fata kamar kurajen jiki,qaiqayi,da sauransu ka nemi man kade sai ka sanya madarar nan ta tumfafiya ka gauraya da kyau ka zanka shafawa bayan kayi wanka.Anti fungal ne mai karfi.

Yana rage yawan faduwa na farfadiya sai a nemi saiwar da 6awon a shanya su bushe.A nemi Karin bayani domin rubutun nada yawa.

Wanda wani 6angare na jikin shi ya mutu ko yake gabda mutuwa (paralysis) to a nemi 6awon
a shanya su bushe,a nemi kitsen damo sai ayi amfani dashi.

Cizon kare sai ayi blending na ganyen sai ya marmasa gishiri ciki a tafasa a zanka wanke wajen da cizon yake.

Kurmantaka sanadin wata rashin lafiya sai a yi blending na ganyen amma wanda ya canza launi ya koma yellow sai a tafasa da kyau a tace ruwan a wanke kunne dasu a bulbula ruwan a ciki a yi haka tsawon sati biyu.za ayi wa Allah godiya.

Ciwon baki dana hakora a tafasa ganyen da shi da fatar lemun tsami sai a marmasa gishiri a rinka wanke baki dashi

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *