Kada Ma aurata Sunyi Wadannan Abubuwan Daf Da Zasu Soma Jimai

Kada Ma aurata Sunyi Wadannan Abubuwan Daf Da Zasu Soma Jimai

kamar komai shine saduwa na ma aurata yana da ka idojinsa Wanda idan har ma aurata zasu bisu zasu samarwa juna yanayin kwanciyar aure mai gamsarwa Rashin yin hakan kuwa na iya hadasa adai yi a hakan
Kada Ma aurata su yi wadannan abubuwan muddin suna da niyar kwanciyar auren a wannan lokacin

Aski Kada ma aurata suyi aske gabansu daf da lokacin da zasu soma gudanar da Jima i

Masana kiwon lafiya sukace hakan zai iya baiwa kwayar cuta damar shiga jikin ma auratan ganin yadda kofar gashinsu yake bude

Haka nan askin yana rage jin dadin wasa da wajen ga ma aurata saboda kaifin da gasun wajen suke da shi na sabon aski Don haka ma aurata sai a kiyaye

Cika Ciki Cin abinci a cika ciki daf da lokacin Jima i bai da kyau ga ma aurata
Hakan na jawo kasala da nauyin jiki Zai iya kuma sa mace amai idan akayi wani yanayin kwanciyar Hakan shi kuma namiji abincin zai rika yawo da girgiza a cikinsa yadda zai yi ta sautin da zai dameshi

Magunguna Mura Duk wani maganin da zai iya saka maye ko kasalar jiki kada Ma aurata su shasu daf da kwanciyar aure
Akwai ma wasu magungunan da zasu iya sa yoyon hanci yadda zai takurawa guda cikin ma auratan Don haka kauracewa sansu shi yafi

Batawa Juna Rai Yana da kyau ma aurata su kasance cikin jin dadi annashuwa da marmarin juna gaf da zasu soma Jimai Amma ba wani cikinsu ya batawa guda rai ba Hakan na iya jawo nakasu a wannan saduwan da zasu yi

Cin Abinci Mai Yaji Wari Ko Doyi Duk wani abincin da yake da karni misali kwai Wari irin kifi albasa ko tafarnuwa basu dace maaurata su cisu ba daf da Jimai Haka nan abinci mai matukar yaji
Duk wani abincin da mutum yaci namiji ko mace yana gangarowa zuwa gabansu Don haka idan mai wari ne suka ci gabansu zai yi wari Wannan yasa masana suka jawo hankalin ma aurata da su kiyaye abubuwan da zasu ci daf da soma kwanciyar Jimai

Wadannan wasu daga cikin abubuwan kaucewa daf da soma kwanciyar aure Da fatan ma aurata zasu kiyaye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *