Innalillahi Wannan Shine Mutumin Daya Kashe Tsohuwar Matar Shi Saboda Yaji Zatayi Wani Auren – Interestingasf

Yadda rundunar yan sandan jihar Adamawa sun cafke wani mutum mai kimanin shekaru 56- a duniya wanda ya bugi tsohuwar matar shi Ƴar kimanin shekaru 38 a duniya, Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ta bayan ya samu labarin cewa za ta yi aure kashe garin ranar da ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

Shidai tsohon mijin nata wanda ake zargi da aikata laifin kisan mai suna, Aminu Abubakar, dake zaune a Unguwar Lelewaji, Shagari Estate a Æ™aramar hukumar Yola ta Kudu an bayyana cewa yaje wurin Nana Fadimatu da misalin Æ™arfe Goma na dare 10pm a ranar Juma’ar nan da ta gabata bayan da ya samu labarin cewa tsohuwar matar tashi zatayi aure.

Sun dai yi aure ne a tsakanin su na kimanin Shekaru Tara Inda suke da Ɗa ɗaya kafin rabuwar su yayin da suke ganawar ne hushi ya ɗebe shi Inda ya riƙa bugunta da wani abu mai nauyi dake hannun shi wanda nan take ta Suma daga baya kuma tace ga garin ku nan.

Yayinda Wanda zai aure ta, Mahmud Rufai, wanda yake zaune a Unguwar Shagari Annex, ya samu labarin sai ya hanzarta kai Maganar ga yansanda na Shagari Police Division, Inda suka damke Wanda ake tuhumar tare da tafiya dashi Offishin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *