Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Yanzu Yanzu Aka Gudanar Da Sallar Gawar Marigayi Sarkin Abaji – Interestingasf

Allah Sarkin yanzu yanzu muke samun labarin yadda aka gudanar da sallar jana’izar sarkin Garin Abaji dake yankin Abuja, Mai Martaba Abdullahi Adamu Ya Rasu Bayan Ya Yanke Jiki Ya Fadi.

Mai martaba marigayi abdullahi adamu abaji ya kasance sarki mai hakuri da tausayin talakawan da yake mulka a garin na abaji, dake cikin yankin babban birnin tarayyar na abuja.

Anyi sallar jana’izar marigayi sarki abdullahi abaji a jiya juma’a 10/3/2023 a cikin babban masallacin garin dake mulki a cikin sa wato abaji, na yankin babban birnin tarayyar nigeria abuja, ubangiji allah yaji kan shi da rahama tare da dukkan musulmai baki daya.

Anyiwa marigayin sallar jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar akan dukkan musulmi idan ya rasu muna fatan allah ubangiji yaji kansa, da rahama idan tamu tazo allah yasa mu cika da kyau da imani ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *