Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Yanzu Wasu Yan Daba Suka Tarwatsa Wani Akwatin Zabe A Kano – Interestingasf

Innalillahi wa’inna’ilaihi raji’un yanzu yanzu muke samun labarin yadda wasu yan zanga zangar siyasa ‘yan farauta suka Tarwatsa Wani Rumfar Zabe da ake gudanarwa yanzu A cikin Birnin Kano.

Yanzu yanzu Abin ya faru anan cikin unguwar Darmanawa ward dake karamar hukumar Tarauni, yayin da suka fasa wasu akwatuna tare da yaga takardar kada kuri’ar zaben da ake tsaka da gudanarwa a halin yanzu.

Wannan al’amarin ya faru ne da safiyar yau karfe tara da minti ashirin 9:20 AM: yayin da ake kan gudanarwa da zaben gwamnoni da yan majalissar jihar kano a yankin na unguwar darmanawa ward dake tarauni kamar yadda majiyar mu ta samu wannan labari da yake faruwa yanzu haka.

Ana zargin rashin fahimta tsakanin ejen din bangarorin jam’iyyar APC da NNPP ne ya jawo wannan rikicin da akayi har takai ga kowa ya janyo anyi asarar akwatin yankin cewar wasu mutane da al’amarin ya faru akan idon su, saidai muce allah ya kyauta allah yasa ayi lafiya agama lafiya ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *