Innalillahi Wa’inna’ilaihi Raji’un Yadda Wasu Dakarun Sojoji Suka Kashe Wasu Yan Ta’adda A Sokoto – Interestingasf

Wasu fusatattun jami’an tsaron dakarun soji a nigeria reshen jihar sokoto sunyi nasarar hallaka wasu manyan yan bindiga sakamakon tarkon da sukayiwa ‘yan bindigar cikin wani kauye dake jihar ta sokoto.

Dakarun Sojojin Nijeriya Sunyi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama a jihar sokoto tare sa kona mafakar su, a yayin da sukayi nasara akan ‘yan ta’addan na jihar sokoto dake nigeria sannan kuma dakarun sojin har yanzu suna yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan jihar sokoto yayi matukar alfahari da samun wannan nasarar da dakarun sojin sukayi akan ‘yan ta’addan dake damun wasu sassan kauyukan jihar a kowani lokaci suka farautar bayin allah dake gefe da jihar ta sokoto cewar gwamna.

Sannan gwamna ya kara dacewa dakarun sojojin zasu kara tsaurara tsattsauran bincike akan kauyukan da suke fuskantar barazana daga wurin ‘yan bindigar domin kawowa karshen su, a kowani lokaci domin samun wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Wasu daga cikin mutanan kauyen da akayi nasarar kubutar dasu daga wurin ‘yan bindigar sunyi matukar godiya ga gwamnatin jihar ta sokoto tare dayi mata fatan alkhairi mai dorewa sannan sunyiwa zaratan sojojin godiya ta musamman tare da fatan nasara a kowani lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *