Innalillahi Wata mummunar gobara ta tashi a cikin kasuwar Gamboru dake birnin Maiduguri sakamakon zargin da akeyi akan ‘yan bindigar da suka addabi yankin birnin jihar ta borno state.
Babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni amma anyi asarar dukiya mai tarin yawan gaske sakamakon gobarar data tashi a cikin kasuwar ta Gamboru dake birnin jihar maiduguri.
Gwamnatin jihar borno tana zargin wasu daga cikin manyan ‘yan bindigar dake damun su, akan faruwar wannan gobarar data tashi sakamakon kwanan baya ma wata gobara ta tashi a kasuwar Monday market, dake birnin maiduguri.
Ana zargin sai zabe ya karo wasu daga cikin al’ummar jihar suke neman tayar da zaune tsaye ta hanyar tayar da gobara cikin kasuwannin jihar ta maiduguri don kada a zauna lafiya domin kada a gudanar da zaben jihar lafiya.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a tsaurara bincike mai tsanani domin gano gaskiyar dalilin daya janyo gobara take tashi yayin da ake kan neman gudanar da zabe a jihar ta maiduguri irin haka tafi faruwa.