‘Yan Bindiga Sun Soma Bin Kauyuka Suna Kwacewa Jama’a Katin Zabe Don Kada Suyi Zaben Gwamna A Cikin Jihar Zamfara.
Labaran da muke samu yanzu haka kauyukan dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara ‘yan ta’adda suna amsar katin zabe a hnnun mutane.
Zuwa yanzu kauyukan da ‘yan bindigan suka shiga sun hada da Kairu, Kyaran, Wawan Icche, Yar Galma duk a karamar hukumar ta Bukkuyum.
Hukumar kula da wallafa labarai ta cikin jihar zamfara karkashin gwamna matawalle na jihar ta bayyana cewa ‘yan bindigar suna neman lalata shirye shiryen zaben da ake neman gudanarwa nan da mako mai zuwa.
Gwamna matawalle ya bayyana cewa kafin a gudanar da zaben a jihar ta zamfara zaiyi kokarin ganin an dakile hare haren ‘yan ta’addan saboda neman kaucewa daga hare haren da suke neman kaiwa.
Yanzu haka dai jami’an tsaron farin kaya a jihar suna gudanar da wani bincike na sirri dangane da irin abubuwan da ‘yan ta’addan suke gudanarwa a jihar kafin zaben gwamna da za’a gudanar a jihar zamfara.