Yanzu yanzu muke samun labari daga jihar borno maiduguri dangane da harin kungiyar boko haram takai musu a sansanin ‘yan gudun hijira dake Dikwa, Inda Ake Zargin Sun Kashe Mutane Kimanin sama da (30) Talatin a cikin sansanin.
Hukumar kula da sansanin ‘yan gudun hijira ta jihar borno ta bayyana wannan lamari daya faru da mutanan a jiya laraba ansamu Hotunan gawarwakin mutanan da aka kashe amma babu kyawun gani.
Gwamnan jihar ta maiduguri babagana umara zulum jajirtaccen gwamna a arewa ya bada umarnin a tsaurara bincike dangane da wannan lamari daya faru na kisan mutanan a cikin sansanin su na yan gudun hijira domin magance matsalar tsaron yankin cewar babagana zulum.
Hakika jihar borno ta kasance daya daga cikin manyan jihohin arewa a nigeria saidai kuma jihar tanakan gaba wurin samun matsalar rashin ingantaccen tsaro daga wurin gwamnatin tarayya domin itama yakamata tana taimaka mana da magance matsalar tsaro a jihar ta Maiduguri.