Innalillahi Wa’inna’ilaihi Raji’un Yadda Al’ummar Ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Rijau A Jihar Neja Ke Gudun Hijira Daga Gidajensu Domin Tsira Daga Harin ‘Yan Bindiga
Allah Ya Kawo Muku Ɗauki Daga Wannan Musifa Ta ‘Yan Bindiga Da Suka Addabe ku hakika wannan wata jarrabawa ce dake kan dukkan wani bawa musamman mutanan mu na arewa dake fama da irin wannan matsaloli na ‘yan ta’adda a kasar nan.

Yanzu haka jama’ar dake wannan kauye na jihar ta Neja suna famar guduwa da iyalan su, domin ganin sun tseratar da rayuwar su daga hare-haren ‘yan bindigar da suke fama dashi a yankin nasu hakika wannan ba sabon abu bane a yankin saidai muce allah ya kyauta.
Wasu daga cikin mutanan kauyen yanzu haka suna guduwa da iyalan su, izuwa wasu wuraren domin tseratar da rayuwar su daga mutuwa ta hanyar farmakin da ‘yan bindigar yankin suke kawo musu a kowani lokaci bayan lokaci a yankin nasu na jihar neja.
Tuni dai yanzu gwamnatin jihar ta neja state ta bada umarnin cewa a gaggauta ganowa mutanan dake da hannu cikin wannan lamari da yake yawan faruwa na kaiwa al’ummar yankin hare hare lokaci bayan lokaci domin samar musu da zaman lafiya a muhallan su.