Innalillahi Wa’Inna’ilaihi Raji’un Allah Yayiwa Malamin Addinin Musulunci Rasuwa A Jihar Katsina – Interestingasf

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Yanzu Yanzu Muke Samun Wani Mummunan Labarin Daya Faru Na Rasuwar Shugaban Kungiyar Sakataren Ƙungiyar Fitayanul Islam Na Jihar Katsina Ya Rasu Sakamakon Hatsarin Mota.

Allah Yayiwa Babban Malamin Addinin Musulunci A Jihar Katsina Kuma Sakataren Ƙungiyar Fitayanul Islam Reshen Jihar Katsina, Sheikh Nasiru Ilallah Funtua Rasuwa Sakamakon Hatsarin Mota Da Ya Rutsa Da Shi Yau Litinin Akan Hanyarsa Ta Zuwa Katsina.

Allah Ya Jikansa Da Rahama hakika wannan mutuwa ta marigayi sheik nasiru ilallah funtua, tayi matukar girgiza mutanan jihar katsina da kewayenta domin kuwa malamin ya kasance mutum mai saukin kai, mai son cigaban al’ummar yankin dama jihar ta katsina baki daya.

Sannan marigayi shiek nasiru ya kasance mutum mai hakuri da juriya da sanin yakamata da kuma kaunar al’umma da yake hakika jihar katsina dama arewa maso gabas sunyi matukar wannan babban rashin na malamin addinin musuluncin dake garin na funtua, allah yayi masa rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *