Innalillahi Wa’inna’ilaihi Raji’un Allah Yayiwa Fatima Rasuwa Ma’aikaciyar Gidan Premier Radio Interestingasf

Innalillahi wa’inna’ilaihi raji’un allah sarki yanzu yanzu allah yayiwa ma’aikaciyar Gidan Rediyon Premier Dake Kano, Fatima Abubakar Dambatta Rasu da safiyar yau laraba a garin jihar kano.

Matar mai suna Fatima ta kasance daya daga cikin manyan ma’aikatan babban sahin labarai da alamuran yau da kullum na na gidan radio Premier dake cikin birnin jihar kano dake nigeria.

Marigayiya Fatima Dambatta ta rasu ne a daren jiya Talata wayewar yau, laraba bayan fama da rashin lafiya ta wani lokaci fatima ta kasance ma’aikaciya mai tarin kwazo da mayar da hankali akan ayyukanta kowace rana.

Za’ayi mata sallar jana’izarta a safiyar yau Laraba da kafe 9 na safe, a unguwar Hotoro Tsamiyar Boka, daidai Farin Gida, dake jihar kano hakika munyi rashin fatima ma’aikaciya mai hazaka a gidan radio na premier radio.

Muna rokon Allah ya jikanta, Allah yasa aljanna makomarta mu kuma da muka rage ubangiji allah yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da imani, allah ya baiwa yan uwa hakuri tare da al’ummar duniya baki daya.

A madadin hukumar gudanarwar Premier Radio da ma’aikatan mu baki daya muna mika ta’aziyya ga Iyalai da yan uwa da al’umma akan rashin Fatima Abubakar Dambatta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *