Innalilahi Wa’inna’ilaihi Raji’un Yadda Wasu Yan Bindiga Sukayi Garkuwa Da Mutane A Katsina Tare Da Kashe Wasu – Interestingasf

Wasu Yan Bindiga da ba’asan ko suwaye ba sun tare wata babbar Motar (KTSTA) Sun Kashe wasu bayin allah Fasinjojin cikin motar Tare Da Raunata Wasu daga cikin bayin allah.

Wasu ‘yan bindiga sun tare motar hukumar Sufuri ta jihar Katsina (KTSTA) inda suka kashe kashe fasinjoji tare da tafiya da kusan mutun 9 cikin daji, tare da raunata wasu a cikin motar a garin Dutsen kura.

A rahoton da muka samu ฦดan bindigar sun yin Garkuwa da Fasinjojin (KTSTA) ne akan hanyar su ta zuwa ฦ™aramar hukumar Batsari bayan tasowar su daga cikin birnin jihar Katsina state dake nigeria.

Wannan lamarin ya faru ne ayau da misalin karfe 3:00 na yammaci jiya ranar Alhamis a daidai Dutsin Kura a hanyar zuwa Batsari dake jihar ta katsina hakika batun yanzu ba irin wannan abu yake faruwa ba cewar wasu bayin allah mazauna jihar katsina.

Jama’ar yankin batsari sunyi matukar allah wadai dangane da wannan lamari daya faru da ‘yan uwansu musulmai, domin hakan bai dace ba wanda suna kallon hakan tamkar gwamnati da jami’an tsaro basa iya kula da al”ummar jihar ta katsina.

Mutanan sun shaida mana cewa jihar katsina tana daya daga cikin jihar da take yawan fuskantar matsaloli lokaci bayan lokaci wanda ganin hakan yasa al’ummar jihar suke ta kuka dangane da irin abubuwan dake faruwa dasu musamman talakawan jihar allah ya kawo musu dauki ameen.

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *