Illolin karas 5 ga jikin ɗan adam da ba kowa ya sani ba:

Idan ana magana a kan abinci masu inganta lafiya, mafi yawancin lokuta ganye da kayan lambu suna daga cikin wadanda aka fi ambatta kamar yadda binciken kimayya da likitoci suka gano.

Sai dai duk da dimbin amfanin da ke tattare da kayan lambun wasu lokutan akwai wasu illoli da mutane da dama ba su san da su ba.

Hakan yasa za mu lissafa tare da yin takaitattun bayani a kan wasu illoli da cin karas ka iya kawo wa ga jikin dan adam kamar yadda The Guardian ta wallafa. Karas.

  1. Yana dauke da sukari mai dimbin yawa Ya kamata mutane da ke da cutar sukari da aka fi sani da diabetes su yi taka tsan tsan game da cin karas domin yana dauke da sukari mai yawa.

Jikin dan adam na sauya sukarin da ke cikin karas zuwa glucose wanda shi kuma ke kara adadin sukarin da ke jinin dan adam cikin gaggawa.

Idan ya zama dole mai ciwon diabtes zai ci karas, ya fi dace wa ya dan dafa karas din kuma ya ci kadan.

  1. Ya kan janyo cutar Carotenemia Karas na dauke da sinadarin beta carotene wanda jikin dan adam ke sauya ta zuwa Vitamin A.

Cin karas fiye da kima ya kan saka sinadarin carotene ya yi yawa a jinin mutum sai ya janyo cutar Carotenemia wacce ke saka fatar mutum ta koma launin ruwan dorawa.

  1. Ya kan janyo kurarraji, gudawa da ‘borin jini’ Akwai wasu mutane da jikinsa baya son karas, idan sun ci karas din su kan gamu da matsaloli kamar kurarraji a fatarsu, gudawa, kaikayin jiki, kumburin jiki da sauransu.

Akwai wata sinadari da ke janyo wannan matsalar da ake samu a ganyen karas din.

  1. Ya kan yi wa jarirai illa Wasu bincike da masu nazarin kimiyya suka gudanar ya nuna cewa bai dace a rika bawa kananan yara karas ba.
    Hakan yasa idan ya zama dole sai dai a bawa yara dan kadan.
  2. Karas na canja dandanon nonon mai shayarwa A lokacin da mace ke shayarwa, duk abinda ta ci ya kan sauya dandanon ruwan nonon ta.

Ya kamata mata masu shayarwa su takaita cin karas domin bincike da dama sun nuna karas na canja dandanon nonon mai shayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *