Idan Mace Na Maka Soyayya Na Gaskiya Zaka Sameta Da Wadannan Abubuwan:

Cikin sauki ka ke iya fahimtar mace idan tana sonka. Kamar yadda zaka iya fahimtar ta idan bata yinka.

Ga wasu alamu na zahiri da zaka iya fahimta daga macen da take maka soyayya na gaskiya.

1: Kishinta zai bayyana akan ka
2: Zata rika kula da abunda baka so da wanda kake so.
3: Kudinka baya gabanta
4: Ba zata taba baiwa wani namiji dama a kanta ba.
5: Bazata bari ka rika ganin bacin ranta ba.
6: Tana iya yin komai saboda Kai
7: Zata rika baka shawaran yadda zaka ci gaba.
8: Bata da hakurin jin ana aibataka.
9:Tana son tasan halin da kake ciki a ko yaushe.
10: Takan shiga tashin hankali akan duk wani abu mara dadi da ya sameka.

Wadannan wasu daga cikin abunda zaka yi la’akari da su idan mace na sonka, so na gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *