Idan Kwankwaso Bai Fita Harka Taba Zan Iya Hallaka Shi Tare Da Mabiyan Shi Ado Doguwa

Honourable alhasan ado doguwa daya daga cikin mutanan da suke cikin majalissar wakilai dake birnin tarayya dan asalin jihar kano dake local government, na mudubi yayi martani akan ‘yan kwankwasiyya na jihar kano.

Ban taba rike bindiga ba kuma ban ma san yadda ake riketa ba, haka kuma ban taba daukar makami ba aduk lokacin zabe, cewar honarabul Alhassan Ado Doguwa Yayin Da Yake Musanta Zargin Da Ake Yi Masa Na Hannu A Kisan Da Aka Yi A Zaben jihar Kano.

Cikin wani takaitaccen bidiyo daya karade shafukan sada zumunta anga wani video, na honourable alhasan ado doguwa dan majalissar tarayyar nigeria, yana fadar munanan kalamai akai ‘yan jam’iyyar (NNPP) ta jihar kano dake nigeria.

Doguwa ya bayyana cewa wasu mutane daga cikin jam’iyyar (NNPP) karkashin Engineer Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso suna zargin shi da kisan da akayi kafin gudanarwa da zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Ya kara dacewa shi kansa rabi’u musa kwankwaso bai isa yayi masa wani abu ba hasalima idan bai fita a rayuwar shiba, tabbas komai zai iya faruwa dashi gargadin honourable alhasan ado doguwa ga kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *